Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya buƙaci ’yan Majalisar Dattijai na Nijeriya da su sake duba tsofaffin dokoki a fannin yaɗa labarai da ke gaban majalisar dokokin ƙasar domin samun damar biyan buƙatun zamani.
Ministan ya bayyana cewa matsalolin da ake fama da su a ƙarƙashin ma’aikatar sun samo asali ne daga tsoffin dokoki.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar Suleiman Haruna ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa ministan ya yi wannan roƙo ne a yayin wata tattaunawa da ‘yan kwamitin Majalisar Dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a a zauren majalisar.
Babban aikin ma’aikatar, a cewarsa, shi ne tabbatar da samar da sahihin bayanai masu inganci a kan ayyukan gwamnati, da shirye-shirye, da ayyuka ga ‘yan Nijeriya, yana mai cewa an ƙara wa ma’aikatar kula da al’amuran aasa gaba saboda taɓarɓarewar ɗabi’u a shekarun da suka gabata, wanda hakan ya sanya ‘yan Nijeriya suka samu damar yin amfani da tsarin ƙasa da ƙasa, wanda kuma hakan ya zama abin damuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya yi watsi da tunanin ‘yan Njeriya cewa ma’aikatar farfaganda ce kawai ta gwamnati, yana mai cewa za a yi amfani da dabarun sadarwa wajen yaɗa bayanai domin amfanin dukkan ‘yan Nijeriya.
Ya kuma bayyana vangarorin da ya yi imanin cewa Majalisar za ta iya tallafa wa ma’aikatar, da suka hada da sake duba dokokin ba da dama ga ma’aikata, waɗanda tuni suke gaban Majalisar Dokoki ta ƙasa, da ingantaccen kasafin kuɗi don baiwa ma’aikatar damar gudanar da gagarumin aikinta, da kuma tallafa wa a kafa Cibiyar Yaɗa Labarai da Ilimi ta Duniya da UNESCO ta amince da ita.
Ya bayyana farin cikinsa da yadda shugabancin kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ya nuna sha’awar mayar da ma’aikatar yaɗa labarai ta tarayya kan gaba wajen wayar da kan jama’a ta ƙasa, ya kuma yi kira da a cigaba da bayar da haɗin kai daga majalisar domin baiwa ma’aikatar nasara a aikin ta.
Ministan ya yi amfani da wannan damar wajen sanar da Majalisar Dattijai buƙatar ma’aikatarsa ta ƙaddamar da “Kamfen ɗin ’Yan Ƙasa,” wanda zai samar da hanyar tattaunawa mai ƙarfi game da ‘yan ƙasa, kishin ƙasa, da kuma ɗabi’u.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Sanata Emeka Kenneth Eze, ya yabawa Ministan kan ayyukan da ya fara, ya kuma jajirce kan buƙatar Ma’aikatar ta kasance mai ƙirƙire-ƙiraire da fasahar ƙere-ƙere da kuma samar da kuɗaɗen shiga maimakon dogaro da sabbin fasahohi.
Ya yi alƙawarin cewa kwamitin zai yi aiki kan gyare-gyaren da ake yi a kan dokokin da za su ba da damar yin aiki tare da tallafa wa ma’aikatar don gudanar da ayyukanta.
Tawagar ministar zuwa majalisar dokokin ƙasar ta haɗa da Daraktoci da shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar.
