Ba za mu bari a yi zanga-zanga a Kano ba – ‘Yan Sanda

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta yi gargaɗin ba za ta bari a gudanar da zanga-zanga a jihar ba, walau ko don goyon bayan hukuncin kotu, ko kuma don adawa da hakan.

Rundunar ta yi wannan gargaɗi ne musamman ga magoya bayan jam’iyyun NNPP da APC a Kano, inda aka ce magoya bayan jam’iyyun biyu sun shirya gudanar da zanga-zanga a jihar a ranar Asabar.

An ce, yayin da magoya bayan NNPP za su yi zanga-zanga ne don nuna rashin yarda da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke nasarar Gwamna Abba, su kuwa ‘yan APC za su yi tasu zangazanga ne don goyon bayan hukuncin wanda ya nuna Yusuf Gwawuna ne ya ci zaɓe.

Sai dai duk da gargaɗin na ‘yan sanda, ɓangarorin biyu sun ce babu abin da zai hana su yin zanga-zangar a ranar Asabar kamar yadda suka shirya.

Rundunar ta ce za ta hukunta duk wanda ta kama yana tada ƙayar baya a jihar.

Gargaɗin Rundunar na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a, ta bakin Kakakinta, SP Abdullahi Haruna a madadin Kwamaishinan ‘Yan Sandan Jihar, Husaini Gumel.

By Editor