Daga UMAR GARBA a Katsina
Ɗaya daga cikin ɗalibai mata biyar na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma, wato FUDMA, a Jihar Katsina da varayin daji su ka sace ta kuvuta daga hannun ‘yan bindigar bayan shafe kwanaki hamsin su na garkuwa da ɗaliban.
Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya, NAN, ya ce ɗalibar ta samu ‘yanci ne bayan da varayin suka sake ta, inda suka ajiye ta a wani gari da ake kira Kunci Kalgo dake qaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara daga nan ne kuma aka dawo da ita gida Katsina.
Yanzu haka dai ɗalibar wadda ba a bayyana sunanta ba ta na asibiti idan take karvar magani.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya tabbatar da sakin yarinyar wadda ta na daga cikin ɗalibai mata biyar da ‘yan bindigar suka sace tun ranar 3 ga watan Ogasta, 2023.
Idan za a iya tunawa Manhaja ta kawo labarin yadda ‘yan bindigar ɗauke da muggan bindigogi suka kutsa kai a wani gida, kusa da makarantar Mariamo Ajiri a ƙaramar hukumar Dutsinma inda ɗaliban ke haya, misalin ƙarfe biyu na dare suka kuma yi awon gaba da ɗaliban jami’ar ta FUDMA.
Sai dai a kwanakin baya rundunar ‘yan sanda a jihar, ta sanar da cewa an kama wanda ake zargin shi ya bai wa ɓarayin dajin bayanan sirrin da suka kai ga sace ɗaliban, sai dai tun daga lokacin rundunar ‘yan sandan ba ta sake fitar da wani bayani ba dangane da sace ɗaliban.
