Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya ta ce hana ta ƙwace mata zaven da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka.

Wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami’i mai binciken kuɗi na jam’iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Ƙasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi iƙirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunƙurin yi wa zaɓen mafi rinjayen al’ummar Kano zagon ƙasa.

‘Ya’yan jam’iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf.

A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam’iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).

Suna dai nuna ɓacin-rai ne kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun ƙorafin zaɓe da kuma ta ɗaukaka qara suka yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Kano, da ya bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, gaskiya.

Ladipo Johnson ya ce tuni hankula suka tashi a Kano yayin da mutane ke ganin cewa an yi musu maguɗi a zaven 2019.

Ya ce jam’iyyar ba za ta yi wasa da ainihin takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba “kuma za mu yi duk abin da ya kamata bisa tsarin doka domin ƙwato abin da duniya ta sani cewa na mu ne.

“Yayin da NNPP ta garzaya zuwa Kotun Ƙoli don bin kadinsu, mun damu da batun zama lafiya, musamman na jihar Kano da kuma Arewacin Nijeriya baki-ɗaya. Don haka, muna son Kotun Ƙoli da ta yi adalci wajen dawowa da al’ummar jihar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf nasara.

“Yayin da muka tinkari kotun ƙarshe, hankula sun tashi a Kano. Kowane lungu-lungu da saƙo na jihar na cike da vacin-rai, inda batun hukuncin kotun ya zama batun da ake tattaunawa a ko’ina, musamman kan tituna, ofisohi, da gidaje,” inji NNPP.

NNPP ta ce tana son faɗa wa shugabannin duniya cewa abin da ake shirin yi ba abu ne mai kyau ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da Afirka da kuma duniya bakiɗaya.

“Yunƙurin ƙwace wa al’umma nasara a Kano zai haifar da sakamako kan al’amuran siyasa, tattalin arziki, da kuma rayuwar mutanen jihar,” inji jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ƙungiyar gwamnonin Arewa, ƙungiyar sanatocin Arewa, ƙungiyar ‘yan majalisar wakilai na Arewa, ƙungiyar shugabannin majalisun dokokin jihohi na Arewa, ƙungiyar Kiristoci na Arewa, da kuma Malamai daga jihohi 19 na Arewa, da su janyo hankalin shugaban ƙasa da Kotun Ƙoli wajen tabbatar da cewa an yi wa jam’iyyar da kuma al’ummar Kano adalci.

By Editor