Siyasa

NNPP da LP sun bayyana matsayarsu kan APC

NNPP da LP sun bayyana matsayarsu kan APC

…Bayan Atiku ya nemi a yi wa jam’iyyar taron dangi*Ko a jikinmu, cewar APC Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar LP ta bayyana ƙudurin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, a matsayin shawara mai kyau da ya kamata a yi la’akari da ita. Sai dai ɗaya jam’iyyar adawa ta NNPP ta ce, za ta iya amincewa da ƙudurin ne kawai idan Atiku zai goyi bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, domin ya ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a 2027. Manyan jam’iyyun adawa na mayar da martani ne kan kiran da Atiku ya…
Read More
Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Abba Gidada

Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Abba Gidada

*Ta ce Abba bai cancanci tsayawa takara ba Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta bi sawun takwararta ta Sauraren Ƙararraki Zaɓen Kano wajen soke nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan jihar. A ranar 20 ga Satumba Kotun Sauraren Ƙararrakin ƙarƙashin jagorancin Alƙali Oluyemi Akintan Osadebay, ta soke nasarar Abba tare da bayyana Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan zabtare ƙuri'u 165,663 daga adadin ƙuri'un da Yusuf ya samu a zaɓen a matsayin ƙuri'u mara amfani kasancewar ba su ɗauke…
Read More
Ya za ta kaya a shari’ar zaɓen gwamnan Kano?

Ya za ta kaya a shari’ar zaɓen gwamnan Kano?

*Yau Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke hukunci Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun Ɗaukaka Ƙara ta saka yau Juma'a, 17 ga Nuwamba, 2023, a matsayin ranar yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnan Jihar Kano ya ɗaukaka, inda yake ƙalubalantar soke nasarar zaɓensa da kotun zaɓen jihar ta yi kwanakin baya. Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya garzaya gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ne bayan kotun ƙorafin zave ta Jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba ta rushe nasarar da ya samu a babban zaɓen 2023, inda ta ce abokin takararsa na Jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, ne halastaccen…
Read More
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan Jihar Zamfara, a matsayin wanda ‘bai kammala ba’. A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari'a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaɓen Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023. Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum. Ta ce, kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Jihar Zamfara, ba ta yi la’akari…
Read More
Buhari ya taya jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen gwamna a jihohin Imo da Kogi

Buhari ya taya jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen gwamna a jihohin Imo da Kogi

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ta ya jam'iyyarsa ta APC murnar lashe zaɓukan gwamna da hukumar zav'ɓe mai zaman kanta ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Buhari ya gode wa al'umar jihohin biyu bisa amincewa da sake ba wa jam'iyyar ta APC dama a jihohin. Tsohon shugaban ƙasar ya kuma gode wa shugabannin jam'iyya da kuma ma'aikata wax'ɗanda su ka yi aiki ba dare ba rana don tabbatar da sake zaɓen Hope Uzodimma na jihar Imo da kuma Usman Ododo a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kogi. Daga ƙarshe, Buhari ya yi…
Read More
Zaɓen Bayelsa: Gwamna Diri ya yi ta-zarce

Zaɓen Bayelsa: Gwamna Diri ya yi ta-zarce

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar Jam'iyyar PDP, Gwamna Douye Diri, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Bayelsa. Da wannan, Diri ya samu yin ta-zarce ke nan inda zai cigaba da shugabancin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa. Diri ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 175,196, sannan ɗan takarar Jam'iyyar APC, Sylva, ya rufa masa baya da ƙuri'u 110,108. Sai kuma ɗan takarar Jam'iyyar LP wanda ya zo na uku da ƙuri' 905.
Read More
Zaɓen Gwamnan Kogi: INEC ta bayyana lokacin da za ta sake zaɓe a wasu mazaɓu

Zaɓen Gwamnan Kogi: INEC ta bayyana lokacin da za ta sake zaɓe a wasu mazaɓu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ya zuwa ranar Asabar mai zuwa za ta sake zaɓe a wasu mazaɓu da aka dakatar da zaɓensu yayin zaɓen gwamna a Jihar Kogi. Ta ce za a sake zaɓen ne a unguwanni guda tara da ke mazaɓar sanata ta tsakiya a jihar. Wuraren da aka dakatar da zaɓen suna yankin Ƙaramar Hukumar Ogori/Magongo ne a jihar. Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ya bayyana a ranar Lahadi cewa, za a sake gudanar da zaɓen a mazaɓun da lamarin ya shafa ne a ranar 18 ga Nuwamba daidai da Sashe…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: INEC ta ayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Imo

Da Ɗumi-ɗumi: INEC ta ayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Imo

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar APC a Jihar, Hope Uzodimma, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da ya gudana a jihar a ranar Asabar da ta gabata. A cewar baturen zaɓen da ya jagoranci tattara sakamakon zaɓen, Abayomi Fasina, Uzodimma ya lashe zaɓen ne da ƙuri' 540,308. Yayin da ɗan takarar Jam'iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, ya rufa masa baya da ƙuri'u 71,503. Ɗan takarar Jam'iyyar LP, Sanata Athan Achonu ne ya zo na uku a zaɓen inda ya tsira da ƙuri'u 64, 081.
Read More
An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Kogi sun ce wani mai suna Umar Hassan ya rasa ransa bayan da aka harbe shi da bindiga a wajen zaɓen gwamna da ke gudana a jihar. MANHAJA ta kalato cewa, hakan ya auku ne ranar Asabar a rumfar zaɓe ta Agala Ogane a yankin Anyigba da ke Mazaɓar Sanatan Kogi ta Gabas. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu bayani a hukumance daga ɓangaren hukumomin tsaro kan batun. Wata majiya ta ce wasu da ake zargin 'yan barandan siyasa ne suka yi kisan. Mai magana da yawun Jam'iyyar APC na kwamitin yaƙin…
Read More
Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

•Zaɓen farko tun bayan kafuwar gwamnatinsa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kimanin masu kaɗa ƙuri’a miliyan 5.2 ne za su fito a ranar 11 ga Nuwamba, 2023 don zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi. Adedayo Akinwale, ya yi nazari kan matakin shirye-shiryen alƙalan zaɓe, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa. Yayin da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da Kogi da kuma Imo ke ƙara ƙaratowa a ranar 11 ga watan Nuwamba, jimillar mutane 5,409,438 da suka yi rajista a jihohin uku ke shirin zaɓar sabbin shugabannin zartarwa na jihohin uku. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa…
Read More