NNPP da LP sun bayyana matsayarsu kan APC

…Bayan Atiku ya nemi a yi wa jam’iyyar taron dangi
*Ko a jikinmu, cewar APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar LP ta bayyana ƙudurin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, a matsayin shawara mai kyau da ya kamata a yi la’akari da ita.

Sai dai ɗaya jam’iyyar adawa ta NNPP ta ce, za ta iya amincewa da ƙudurin ne kawai idan Atiku zai goyi bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, domin ya ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a 2027.

Manyan jam’iyyun adawa na mayar da martani ne kan kiran da Atiku ya yi, a ranar Talata, na cewa jam’iyyun adawa za su yi haɗaka domin kawar da APC daga mulki.

An rawaito cewa, Atiku ya bayar da shawarar haɗewar ne a lokacin da ya karvi baƙuncin kwamitin zartarwa na majalisar ba da shawara ta jam’iyyu ta Nijeriya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi gargaɗi kan yiwuwar Nijeriya za ta shiga cikin jam’iyya ɗaya.

Ya ce, “duk mun ga yadda jam’iyyar APC ke ƙara mayar da Nijeriya mulkin kama-karya na jam’iyya ɗaya. Idan ba mu haɗu, mun ƙalubalanci abin da jam’iyya mai mulki ke ƙoƙarin haifarwa ba, dimokuraɗiyyar mu za ta sha wahala a kanta, kuma sakamakonta zai shafi al’ummomin da ba a haifa ba.”

A wata hira ta musamman da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, muƙaddashin Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar LP, Obiora Ifoh, ya bayyana kiran na Atiku a matsayin kyakkyawan tsari da ya kamata kowane ɗan Nijeriya ya yi la’akari da shi.

Ifoh ya ce, “Kiran Atiku shawara ce mai kyau, kuma ya kamata kowane ɗan Nijeriya ya yi la’akari da shawarar a matsayin mai kyau da ake son a kawar masu mayar da Nijeriya baya da ke mulki saboda su ba ‘yan dimokraɗiyya ba ne.

“Kowane ɗan Nijeriya yana sha’awar samun dimokraɗiyya ta gaskiya. Abin da muke da shi a yanzu ya yi nisa da dimokuraɗiyya. Don haka, idan akwai wata magana da ’yan adawa suka yi don tabbatar da cewa an dawo da dimokuraɗiyya, me zai hana?

Dole ne a yi tunani mai kyau game da wannan magana. Duk wani abu da zai sa ‘yan Nijeriya su shaida dimokraɗiyya, dole ne a yi shi.”

Amma jam’iyyar NNPP ta bayyana kiran na Atiku a matsayin abin tausayi da shan magani bayan mutuwa.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar na Ƙasa, Yakubu Shendam, ya ce, duk haɗewar ba za a goyi bayan Kwankwaso ya zama Shugaban Ƙasa ba, to NNPP ba ta da sha’awar shiga.

Shendam ya ce, “wannan kamar magani ne bayan mutuwa. Mu na tafiya gabaɗaya saboda mu na da “magudu” wanda ke da ikon ƙwace Nijeriya.

“Mun yi imanin cewa, akwai buƙatar yin taho-mu-gama don neman goyon baya daga mutane don cin zaɓe, daga kowane vangare. Sai dai mun yi imanin Kwankwaso mai hannu ɗaya zai iya ceto Nijeriya a 2027.

A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar APC mai mulki ta ce ko a jikinta, domin amincewa da ƙudurin da Atiku ya yi na jam’iyyun adawa su haɗa wajen yaƙar jam’iyyar mai mulki, hakan ba barazana bane a gare ta.

Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce, “Ta yaya kuma me ya sa za a yi mana barazana? Atiku dai an yi masa shara a kotu tare da yi masa shara a idon jama’a.

Ta wace hanya ce Atiku da jam’iyyarsa ke da hanyar sanya barazana a zukatan jam’iyya mai mulki?