Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Abba Gidada

*Ta ce Abba bai cancanci tsayawa takara ba

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta bi sawun takwararta ta Sauraren Ƙararraki Zaɓen Kano wajen soke nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan jihar.

A ranar 20 ga Satumba Kotun Sauraren Ƙararrakin ƙarƙashin jagorancin Alƙali Oluyemi Akintan Osadebay, ta soke nasarar Abba tare da bayyana Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan zabtare ƙuri’u 165,663 daga adadin ƙuri’un da Yusuf ya samu a zaɓen a matsayin ƙuri’u mara amfani kasancewar ba su ɗauke da sanya hannun Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Daga bisani, rashin gamsuwa da hukuncin kotun ya sanya Abba ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara don kare kujerarsa.

Sai dai kuma, a ranar Juma’a, 17 ga Nuwamban 2023, Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ke yanke hukunci kan Zaɓen Gwamnan Kano, ta ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP bai cancanci tsayawa takara ba a Zaɓen Gwamnan Kano da aka gudanar a watan Maris.

Kotun mai zamanta a Abuja, ta jaddada hukuncin Alƙalan Kotun Sauraron Ƙararrakin da suka tabbatar cewa babu sunan Abba a rajistar ’ya’yan da Jam’iyyar NNPP ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), don haka bai cancanci tsayawa takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ba.

An dai gudanar da zaɓen ne tun a wata Maris, inda Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai daga bisani jam’iyyar APC ta garzaya Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe, tana mai neman a sake nazari kan lamarin, inda ta samu nasara kotun ta ce ɗan takararta, Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaɓen.