An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Kogi sun ce wani mai suna Umar Hassan ya rasa ransa bayan da aka harbe shi da bindiga a wajen zaɓen gwamna da ke gudana a jihar.

MANHAJA ta kalato cewa, hakan ya auku ne ranar Asabar a rumfar zaɓe ta Agala Ogane a yankin Anyigba da ke Mazaɓar Sanatan Kogi ta Gabas.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu bayani a hukumance daga ɓangaren hukumomin tsaro kan batun.

Wata majiya ta ce wasu da ake zargin ‘yan barandan siyasa ne suka yi kisan.

Mai magana da yawun Jam’iyyar APC na kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da aukuwar hakan, kana ya yi tir da hakan tare da kira ga jami’an tsaro a yankin da su gaggauta binciko waɗanda ke da hannu a kisan.