Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin masarufi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a cikin makon da ya gabata ya kai ziyarar bazata ga wasu kasuwanni dake cikin birnin Bauchi da kewayenta domin ganewa kansa yadda ‘yan kasuwa suke zuga farashin kayayyakin masarufi da zumar yi masu nasihar ta natsu.

Yayin ziyarar ta bazata, Mai Martaba Sarkin ya kekkewaya kasuwanni da suka haɗa da wacce take Wuni, Muda Lawal da kuma ta Wajen Durum dake wajen gari, inda yayi hulɗoɗi da ‘yan kasuwa domin ya jiyewa kansa ire-iren farashin kayayyakin masarufi, husasan ma masara, dawa, gero, alkama, da dai sauran su.

Dokta Rilwanu Suleiman Adamu ya kewaya sassa daban-daban na kasuwanni da ya ziyarta, yana mai bayar da shawarwari dangane da buqatar sauqaqa farashin kayayyakin masarufi domin ragewa talaka raɗaɗin rayuwa da yake ciki a wannan yanayi da wasu mutane suke yin kasuwanci idanuwansu a rufe saboda kwaɗayin tara kuɗaɗe, yaki halal, yaki haram.

Yayin kewaya kasuwannin dama ‘yan kasuwa, Mai Martaba Sarkin Bauchi ya kuma shawarce su da su riqa cika mudu, har ila yau, wajibi ne suyi amfani da mudu wanda gwamnati ta amince dashi, domin kamar yadda ya lura, wasu ‘yan kasuwa suna cinikayya ne da ƙaramin mudun awu, wasu ma basu cika amintaccen mudun yadda ya kamata.

Mai Martaba Sarkin Rilwanu, a cikin ziyarar tasa, shima ya auni wasu kayayyakin masarufi domin amfanin iyalinsa, yana mai ƙara shawartar ‘yan kasuwa da su riƙa rage farashin kayayyakin aminci domin kyautata wa talaka, da kuma neman falalar Ubangiji Maɗaukaki.

Ya kuma bai wa ‘yan kasuwa tabbacin cigaba da yin irin wannan ziyara ta gani da ido, domin ganin yadda ‘yan kasuwa za su riqa rage zalamar tara kuɗaɗe ta hanyar tsauwala wa jama’a farashin kayayyakin masarufi a dukkan kasuwanni dake cikin masarautarsa.

Dokta Rilwanu Adamu, ya kuma ziyarci sashin mahauta inda ya bukace su dasu kula da tsafta da lafiyar nama, da tsaftace farfajiyoyi ko wuraren kasuwancin su, yana mai cewar, tsafta tana daga cikon addini, kuma tsaftace wa yana inganta lafiyar al’umma.

‘Yan kasuwa a kasuwanni dabam-dabam da Mai Martaba ya ziyarta, sun yabawa Sarki matuƙa gaya, suna masu bayyana ziyarar a matsayin wani nunin kyakkyawan tsarin shugabancin ne wanda za su yi koyi dashi, suna masu bukatar ɗorewar irin wannan ziyara domin su cigaba da amfana.

‘Yan kasuwan, sun kuma jaddada godiyar su wa Sarkin Bauchi bisa ƙoƙarin da na nusar da irin wannan tsari na shugabanci, daya kasance misali ga na baya, dama ɗaukacin talakawa baki ɗaya, suna masu addu’ar Allah yaja zamanin Sarki Rilwanu Suleiman Adamu domin su cigaba da cin gaskiyar wannan salon tsarin shugabancin sa.

Sun kuma jaddada goyon baya da biyayya su wa Mai Martaba Sarkin da majalisar sa, kamar yadda suke yin biyayya da goyon baya ga dukkan hukumomi da masarautu tun daga ƙasa har zuwa sama.