Haƙƙi na ne fitar da Arsenal kunya – Arteta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana cewa, dole ne ya fitar da ƙungiyar kunya a idon duniya bayan wasar da suka lallasa Sevilla da ci 2-0 a gasar Zakatun Turai.

A kwanakin baya ma ya ce, ya zama wajibi ya kare kulob ɗin bayan ya caccaki alkalin wasa a karawar da Newcastle ta doke su da ci 1-0 a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Ya ce, shawarar da aka yanke kan ƙwallon Anthony Gordon a St James’ Park “abin kunya ne” kuma “abin takaici”.

Arsenal ta goyi bayan kalaman Arteta a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wadda tsohon ɗan wasan Manchester United Gary Neville ya kira abu “mai haɗari”.

“Ya zama wajibi gare ni in tsaya a gabanku in bayyana gaskiya ,” inji Arteta a ranar Talata.

“Aikina shi ne kare ‘yan wasana da kuma kulob ɗina ta hanya mafi kyau, abin da nake da niyyar yi ke nan a kowanne lokaci.”

Rashin nasara a Newcastle ya kawo ƙarshen wasan da Arsenal ta yi a gasar Firimiya ba tare da an doke ta ba, abin da ya sa ta zama ta huɗu, inda akwai maki uku tsakaninta da Manchester City da ke jan ragamar teburin.