Pepe ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan baya na Portugal Pepe ya zama ɗan wasa mafi yawan shekaru da ya zura ƙwallo a raga a tarihin gasar zakarun Turai, inda ya ci qwallon da ta taimaka wa FC Porto ta doke Royal Antwerp.

Pepe mai shekaru 40 da kwana 254 da haihuwa, ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Antwerp a minti na 91, inda ya zama ɗan wasa na farko da ya haura 40 da ya zura ƙwallo a gasar.

Francesco Totti ke riƙe da tarihin mai mafi yawan shekaru da ya zura ƙwalo a shekara 38 da kwanaki 59.

Pepe kuma shi ne ɗan wasa mafi shekaru da ba mai tsaron gida ba da ya buga wasa a tarihin gasar.

Ya kafa wannan tarihin ne a lokacin da ya fara karawar FC Porto da Antwerp a ranar 25 ga Oktoba.

Mai tsaron gida Marco Ballotta shi ne ɗan wasa mafi yawan shekaru a gasar Zakarun Turai, yana da shekaru 43 da kwanaki 252 da haihuwa a lokacin da ya buga wa Lazio wasa da Real Madrid a watan Disamban 2007.