An horar da ƙananan ‘yan kasuwa 102 dabarun inganta sana’o’i na zamani

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Ƙwararru kan harkokin kasuwancin da suka fito daga ɓangarori daban-daban sun shawarci ƴan kasuwa da masu ƙananan masana’antu su rungumi sabbin hanyoyin kasuwanci da fasahar sadarwa ta zamani, domin bunƙasa sana’o’insu.

An yi wannan kiran ne a wajen taron da Dandalin Horarwa Kan Dabarun Sana’o’in Zamani na Mu Inganta Sana’armu wanda ya gudana a birnin Kano, da nufin wayar da kan ƙananan ƴan kasuwa, da samar da muhallin da za su baje-kolin sana’o’insu, don sabbin abokan hulɗa da ƙulla ƙawance tsakanin ƴan kasuwa da masu masana’antu.

Taron Mu Inganta Sana’armu wanda shi ne irinsa na huɗu da ake gudanarwa a jere ya fara ne tun daga kafafen sada zumunta har zuwa inda ake gabatar da shi a bayyane, da aka fara a karo na farko cikin shekarar 2020, ƙarƙashin shugabancin Maryam Abbas Bichi. Tun daga lokacin taron yake samun karɓuwa a wajen ƴan kasuwa da masu faɗa a ji a harkokin kasuwanci daga cikin Jihar Kano da wasu sassan arewacin ƙasar nan.

A bana taron ya mayar da hankali ne wajen tattauna fasahohin zamani da ƴan kasuwa za su yi amfani da su, don inganta sana’o’insu, kamar yadda jagoran dandalin Mu Inganta Sana’armu, Maryam Bichi ta bayyana.

Ta ƙara da cewa, “Na fara taron Mu Inganta Sana’armu ne domin samar da wani dandali na taimakawa mata da matasa ‘yan uwana, da suka fara sana’a domin neman mafita ta rashin aikin yi, suka fara sana’a amma basu su san ta inda za su fara ba. Shi ya sa duk shekara muke gudanar da wannan taro don mu horar da su kan abubuwan da suka shafi aiwatar da kasuwanci a zamanance.”

Babban baƙo a taron, Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Kano Shawara Kan Harkokin Fasahar Zamani, Alhaji Yusuf Sharaɗa, ya yabawa jagoran shirya taron tare da shaidar da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan wannan taro, kuma za ta ba da dukkan gudunmawar da ta kamata don ganin ɗorewarsa duk shekara, saboda cigaba kasuwanci da ƙananan masana’antu a jihar, kamar yadda suke ƙoƙarin zamanartar da harkokin tafiyar da gwamnati a harkar ICT.

Daga cikin ƴan kasuwar da suka yi jawabi a taron har akwai Hajiya Aisha Mujahid Yusuf wacce ta ce sun fara sana’ar fura da nono ne a gida, har kuma aka fara sa su suna yin na taro ko biki, kawo yanzu har sun ƙirƙiro da kamfanin sarrafa yogot, fura da nono na zamani da sauransu, kuma yanzu haka tana da ma’aikata shida da ta bai wa aikin dogaro da kai.

Ita ma a nata bayanin, Rabi’atu Kabir Sa’idu manajan kamfanin MAAB Luxury Home dake sayar da kayan alatu na gidaje ta ce wajibi ne mata su kula da kasuwanci da sanya tsoron Allah a cikinsa ta yadda zai qara musu fahimtar juna a tsakaninsu da mazajensu na aure da kuma taimaka musu, ‘yan’uwa da sauran al’umma.

Alhaji Umar Faruq Tabi’u, Wakilin Arewa Gumel ɗaya daga cikin manyan baƙi ya ce, a shirye masarautun gargajiya suke don ganin irin waɗannan ayyuka na tallafawa cigaban al’umma sun samu ɗorewa.

Kamfanoni 102 ne suka yi rijista da baƙi fiye da 600 da suka samu halartar wannan taron na bana.