Har ƙasar Saudiyya muna aikin ciyar da abinci – Hajiya Hannatu

Manhaja logo

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Hajiya Hannatu Tijjani Haruna Shugabar gidan abinci na 7:30 dake Kano, ta bayyana cewa daga kafuwar wannan gida ta horas da dubban mata sana’o’i da irin wannan aiki na gidan abinci kyauta da kuma samar wa mutane musamman matasa maza da mata sama da 3,000 domin su dogara da kansu.

Hajiya Hannatu ta ce yanzu haka tana tare da wasu, inda wasu kuma suka buɗe nasu don tsayawa da ƙafafuwansu sakamakon horon da suka samu a Kiminu Food.

“Don haka ina farin ciki da samun wannan dama daga Ubangiji,” inji ta.

Hajiya Hannatu Tijjani Haruna ta bayyana haka ne lokacin taron bunqasa sana’o’in mata da ya gudana a ranar Litinin ɗin nan ta gabata wanda aka yi a birnin Kano.

Har ila yau ta ce akwai buƙatar mata su rungumi sana’o’i domin taimakawa kansu da iyalansu domin tafi da al’amuran yau da kullum a gidajen aurensu, domin a cewarta “yau tana buƙatar mata da maza kowa ya tashi tsaye wajen neman na halak, wannan ce ma tasa duk shekara nakan sa a nemo mata marasa ƙarfi a horar da su sana’o’i inda nake horas da mata 250 kyauta daga cikin birni da yankunan karkara na ƙananan hukumomi 44 a Kano,” inji ta.

A qarshe ta bayyana cewa “duk wannan cigaba da aka samu wanda har a ko’ina a Nijeriya wannan gidan abinci, har ƙasashen waje irinsu Saudiyya da sauransu muna zuwa yin aikin abinci.