An yi garkuwa da jariri ɗan wata huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jariri ɗan wata huɗu da haihuwa a Jihar Akwa Ibom.

Da misalin ƙarfe 3 na daren Asabar ne wasu ’yan bindiga biyu suka kutsa cikin gidan wani magidanci mai suna Mista Edeme Eyo suka ƙwace jaririn nasu.

Mista Edeme Eyo ya ce maharan da suka zo ɗauke da bindigogi da adduna sun kutsa har cikin uwar ɗakinsu ne suka ɗora musu bindiga a kai da matarsa, suka nemi a ba su jaririn.

A cewarsa, ’yan bindigar sun fi ƙarfinsa, matarsa tana ihu, amma suka ƙwace jaririn daga hannunta suka shiga wata mota da suka zo da ita suka tsere.

Magidancin ya ce wannan abin ya faru ne ba da jimawa ba da ya rasa ɗansa na fari, wanda ya rasu ’yan watanni bayan haihuwarsa.

Iyayen jaririn da ke zaune a ƙauyen Enen-Atai da ke Ƙaramar Hukumar Itu sun roƙi jami’an tsaro su taimaka su ceto musu jaririn nasu daga hannun maharan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John, ya ce rundunarsu tana ƙoƙarin kamo ’yan bindigar da kuma ceto jaririn don miƙa shi ga iyayensa.