Farfesa Sa’adatu ta karɓi ragamar jagorancin Jami’ar Nasarawa a hukumance

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A yanzu haka sabuwar Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake birnin Keffi hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da aka naɗa ta kwanan nan ta kama aiki gadan-gadan.

Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kama aiki a hukumance ne a matsayin mace ta farko da aka naɗa a matsayin sabuwar shugabar jami’ar ta jihar Nasarawa bayan ta karɓi ragamar mulkin jami’ar a hukumance daga gun mai riƙon ƙwaryar muƙamin wato Farfesa Sallau Modibbo wanda shine muƙaddashin shugabar jami’ar ta fannin ilimi a yayin wani zaman karɓan karagar aikin wadda aka gudanar a ofishin sabuwar shugabar a makon da ake ciki.

A jawabinta jim kaɗan bayan ta amshi ragamar jagorar babban jami’ar ta gwamnatin jihar farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yaba wa tsohon shugaban jami’ar Farfesa Suleiman Bala Mohammed da sauran shugabannin jami’ar baki ɗaya a duka matakai dangane da sadaukarwa da riqon amana da suka yi wajen cigaban jami’ar inda ta tabbatar cewa bazata basu kunya ba a yanzu da ta kama aiki a matsayin sabuwar shugabar.

Ta ce maimakon haka za ta yi duka mai yuwuwa ne don tabbatar ta dora daga inda tsofaffin shugabannin suka tsaya kana ta buƙaci haɗin kai da cikakken goyon bayan duka malamai da ɗalibai da sauran ma’aikatan jami’ar baki ɗaya don bata damar sauke nauyin dake wuyanta yadda ya dace.

Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yi amfani da damar inda ta jinjina wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafi da gwamnatinsa ke bai wa jami’ar akai-akai don bunƙasar harkokin ilimi inda ta tabbatar masa da al’ummar jihar baki ɗaya cewa ba za su yi nadamar kasancewarta a matsayin shugabar jami’ar na yanzu ba.

A yayin zaman bayan miƙa takardun kama aikin wa sabuwar shugabar an kuma ɗauki hotuna da zaga don dubu duka ofishoshin sabuwar shugabar da dai sauransu.