NYSC ta yi bikin kammala horar da masu hidimar ƙasa sama da 2,000 a jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An yi kira na musamman ga duka hukumomi da ofishohi daban-daban da ake turo ‘yan hidimar qasa a sassan jihar Nasarawa baki ɗaya su tabbar suna bai wa sabbin masu hidimar ƙasar waɗanda aka turo hukumominsu cikakken kulawa da goyon baya a koyaushe don basu damar gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

Kodinetan hukumar masu hidimar ƙasar wato NYSC a turance na jihar Nasarawa Abdullahi Jiqamshi ne ya yi wannan kira a jawabinsa a wajen bikin kammala horon na bana na rukunin A sama da mutum 2000 wadda aka gudanar a sansanin ‘yan yi wa ƙasa hidimar na Magaji Ɗan Yamusa dake garin Keffi hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa a makon da ake ciki.

Abdullahi Jiqamshi ya ce ba shakka ya zame dole ya yi kiran idan aka yi la’akari da yadda sau da yawa wasu hukumomin da cibiyoyi da ake turo ‘yan bautan ƙasar don aiki sukan jin amsar su tare da nuna musu halin-ko-in kula da sauransu.

Ya kuma yi kira ga su masu hidimar ƙasar da aka horar aka kuma turo su waɗannan sassan jihar ta Nasarawa daban-daban su tabbatar sun gudanar da ayyukansu na hidimtawa ƙasar a wuraren da aka turo su ɗin cikin gaskiya da riqon amana su kuma riqa sadaukar da komai wajen tabbatar sun sauke nauyin dake wuyansu yadda ya dace don cimma burin shirin na hidimar ƙasar a jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Har ila yau Kodinetan Abdullahi Jikamshi ya yi amfani da damar inda ya taya su murnar kammala horon nasu wadda hukumar ta NYSC ta kwashe kimanin makonni 3 tana yi musu inda ya ƙalubalance su su yi duka mai wuya wajen yin amfani da duka abubuwa da aka koya musu a lokacin horarwar a wuraran ayukan nasu dabandaban kana su rika kula da tsaro musamman ta guje wa yin tafiye-tafiye da daddare da sauran su.

Daga nan sai Kodinetan ya kuma yi amfani da damar inda ya jinjina wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jogorancin Injiniya Abdullahi Sule dangane da gagaruman tallafi da yake bai wa hukumar ta ‘yan hidimar ƙasa a jihar inda ya kuma gabatar wa gwamnan da wasu qalubalai da hukumar ke fuskanta a yanzu musamman batun kammala ginin babban dakin taron hukumar dake sansanin wadda a cewarsa idan aka kammala zai ce nesa ba kusa ba wajen inganta harkokin hukumar da sauransu.

A nasa ɓangaren da yake maida martanin jawabin gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule bayan ya taya sabbin ‘yan hidiman ƙasar murnar kammala horarwar su na makonni ukun ya kuma yi kira agaresu su tabbatar suna kasance jakadun hukumar nagari a duk inda suka tsinci kansu kana ya tabbatar musu cewa gwamnatin sa zata cigaba da samar musu da tsaro don kare rayukan su da dukiyoyin su ayayin da suke sauke nauyin dake wuyan su inda ya kuma sanar cewa tuni gwamnatin sa ta amince da aikin kammala ginin na babban dakin taron hukumar ba tare ɓata lokaci ba.

Abubuwan da aka gudanar a wajen taron sun haɗa da fareti da ɗaukar hotuna da sauransu.