CBN ya bai wa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci duk masu sana’ar POS a ƙasar nan da su yi rajistar kasuwancinsu da hukumar kula da harkokin kamfanoni (CAC) nan da watanni biyu.

An bayyana hakan ne bayan wata ganawa tsakanin Fintechs da Shugaban CAC na Ƙasa, Hussaini Magaji (SAN) a Abuja a ranar Litinin.

Shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar wanda zai ƙare a ranar 7 ga watan Yuli, ba an yi ba ne don muzgunawa wata ƙungiya ko ɗaiɗaikun mutane ba, amma “ya yi daidai da ƙa’idojin doka da kuma umarnin Babban Bankin Nijeriya.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar kula da harkokin kamfanoni da kamfanonin Fintech a Nijeriya, waɗanda aka fi sani da PoS operators, sun amince da wa’adin watanni biyu na yin rajistar wakilansu, ‘yan kasuwa da kuma ɗaiɗaikun mutane da hukumar ta CAC bisa ga sharuɗɗan doka da kuma umarnin Babban Bankin Nijeriya.

“An cimma wannan matsaya ne a ranar Talata yayin wata ganawa tsakanin Fintechs da babban magatakardar hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji, a Abuja.