Gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar kafa rundunar ‘yan bijilanti a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana cewa ta tayar da azama wajen yaƙi da ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a duk faɗin jihar, inda ta ce za ta samar da runduna ta musamman don tabbatar da tsaro a duk faɗin jihar. 

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da ya ke bayani game shirin da gwamnatin ta yi na zaƙulo wasu matasa daga Ƙananan Hukumomin jihar 14, waɗanda za su yi aikin samar da tsaro a Hukumar tsaron da gwamnatin za ta kafa mai suna ‘Community Protection Guards (CPG), waɗanda ya ce za a fara ba kashin farko horo a cikin mako guda.  

Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya sanar sa haka a watar sanarwar da ya fitar, inda ya ce Gwamnan ya karɓi rahoton kwamitin ya da kafa na karɓar mulki, wacce Shugaban kwamitin, Tsohon Shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Bello Umar Karakkai ya miƙa. 

Cikin jawabin sa wajen karɓar wannan rahoto, Gwamna Lawal ya yaba wa wannan kwamiti bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen gudanar da aikin, tare da yin la’akari da abubuwan da gwamnati za ta mayar da hankali a kai a cikin wannan rahoto. 

Haka kuma Gwamnan ya gode wa kwamitin karɓar mulkin jihar da waɗanda suka tsara rahoton, musamman bisa yadda suka yi la’akari da fannonin da za a bi don ci gaban jihar Zamfara. 

Daga nan ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta bi abubuwan da al’umma ke buƙata wajen aiwatar da shawarwarin wannan rahoto don samar da ingantacciyar Jihar Zamfara. 

“A shirye gwammati ta ke don aiwatar da wannan rahoto, da zarar an kammala nazarin abubuwan da ya ƙunsa.” inji Kakakin Gwamnan. 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Gwamna Lawal ya ɗauki ƙwararan matakai da azama don aiwatar da shawarwarin.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya Gwamnan Jihar Katsina dake maƙota da Zamfara ya ƙaddamar da makamanciyar rundunar a jiharsa, lamarin da ya kawo yabo daga masu nazari.