Ba mu bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗin Naira ba – CBN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce duk takardun kuɗi (tsofaffi da sababbi) suna nan a kan doka.

Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023.

Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al’umma.

Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira.

“Don kauce wa shakku, yayin da muke nanata cewa akwai isassun takardun kuɗi a faɗin qasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullun, muna so kuma mu bayyana cewa duk wata takardar kuɗi da Babban Bankin Nijeriya, za ta ci gaba da aiki kuma bai kamata a yi watsi da ita ba, kamar yadda yake a sashe na 20(5) na dokar CBN, na 2007.

Babban bankin ya umarci rassansa a faɗin ƙasa da su c gaba da bayar da tsofaffin takardun kuɗi da kuma sababbi don ci gaba da rarrabawa ga abokan hulɗar bankuna.