Matar gwamnan Kebbi za ta haɗa gwiwa da Intel Box don haɓɓaka ayyukan SDGs

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Matar gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasir Idris nemi haɗin gwiwa tsakanin Nasara Foundation da Intel Box a kan muradun ƙarni SDGs.

Ta yi wannan bayani ne a lokacin da ta kai ziyara a ofishin Intel Box Solution Ltd a Abuja babban Birnin tarayyar Nijeriya ranar Talatar da ta gabata.

Ta ce wannan haɗin gwiwar zai yi tasiri wajen inganta rayuwar al’umma ta fannoni da yawa da suka haɗa da ilmin ‘ya’ya mata, horas da makamai kiwon lafiya, mata masu ciki da jinjirai da kuma koyar da sana’o’in hannu ga mata da matasa.

Ta ƙara da cewa yin haka zai zama silar cimma biyan buƙatun shirin ƙasashen United Nations na Sustainable Development Goals a kan kiwon lafiya da kuma ilmi na (SDG3 da SDG4) saboda ya yi daidai da irin ayyukan da Nasara Foundation ke aiwatarwa a jihar Kebbi saboda haka yanzu an samu ƙwarin gwiwa.

Tun farko da ya ke jawabi babban daraktan kamfanin Faisal Lawal ya nuna jin daɗinsa bisa ga ganin an samu hanyoyin da idan an ɗauke su za a cimma nasarori a ɓangarorin kamfanin da kuma Nasara Foundation.