Farfesa a ABU ya maido Naira miliyan 1 da aka biya shi bisa kuskure

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban makarantar horas da sojoji NDA John-Ochefu Ochai a ranar Laraba ya ziyarci Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zariya domin ganawa da Farfesa Umar Ka’oje bayan ya maido da sama da Naira miliyan 1 da aka biya shi bisa kuskure.

Kuɗaɗen da aka biya farfesan sun kai Naira miliyan 1,153,953.36. Waɗannan kuɗaɗen na aikin karantarwa da ya yi ne a NDA aka biya shi haƙƙinsa.

Ochai ya zo Jami’ar tare da wasiƙa godiya da yabo daga NDA wacce ke ɗauke da kwanakin wata 12 ga Satumba, 2023.

Shugabar sashen koyar da kwas ɗin ‘Political Science and International Studies’ Rahanatu Lawal ce ta marabci Shugaban makarantar NDA.

“Mutane ƙalilan ne a yau za su iya yin ƙarfin hali da jajircewar Farfesa Ka’oje wanda ke jaddada irin wannan hali na ƙwarai ya kamata a yi koyi da shi.

Shugaban NDA ya ce ya ziyarci jami’ar tare da wasiƙar yabo domin ƙara nuna godiyarsa ga irin wannan aiki da Farfesan ya yi.

Ochai ya yi albishir cewa NDA za ta karrama Farfesan da lambar yabo nan ba da dadewa ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Ka’oje ya gode wa Ochai bisa wannan ziyara ta karamci da ya yi domin ya gana da shi da kuma jami’ar ABU.

Mutane da dama da suka zanta game da wannan ƙoƙari na Ka’oje sun ce a samu mutum mai imani irin haka zai yi wuya a wannan lokaci da ake fama matsin tattalin arziki a Nijeria, na raɗaɗin cire tallafin da gwamnatin Tinubu ta yi.