Zaɓen Bayelsa: Gwamna Diri ya yi ta-zarce

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Gwamna Douye Diri, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Bayelsa.

Da wannan, Diri ya samu yin ta-zarce ke nan inda zai cigaba da shugabancin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa.

Diri ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 175,196, sannan ɗan takarar Jam’iyyar APC, Sylva, ya rufa masa baya da ƙuri’u 110,108.

Sai kuma ɗan takarar Jam’iyyar LP wanda ya zo na uku da ƙuri’ 905.