Buhari ya taya jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen gwamna a jihohin Imo da Kogi

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ta ya jam’iyyarsa ta APC murnar lashe zaɓukan gwamna da hukumar zav’ɓe mai zaman kanta ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Buhari ya gode wa al’umar jihohin biyu bisa amincewa da sake ba wa jam’iyyar ta APC dama a jihohin.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma gode wa shugabannin jam’iyya da kuma ma’aikata wax’ɗanda su ka yi aiki ba dare ba rana don tabbatar da sake zaɓen Hope Uzodimma na jihar Imo da kuma Usman Ododo a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kogi.

Daga ƙarshe, Buhari ya yi wa sabbin gwamnonin biyu fatan gama mulki lafiya.