Sama da mutum 30 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Taraba

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum 32, ciki har da ƙananan yara su 20 da iyaye 12 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya ritsa da su a garin Ibbi, cikin Ƙaramar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Bayanai sun ce jirgin da ya yi hatsarin ya yiwo jigilar masunta su sama da 50 daga Ibbi da nufin zuwa gabashin Nijeriya.

Hatsarin wanda ya auku a ranar Asabar, ya faru ne a kusa da Zabu da ke iyakar Taraba da Binuwai a Kogin Binuwai.

News Point Nigeria ta rawaito wani mazaunin garin Ibbi, Malam Ibrahim Ibbi, ya ce yara 20 da iyaye 12 ne suka rasa rayukansu a hatsarin.

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana hatsarin a matsayin abin tashin hankali, wanda ya auku ‘yan kwanaki da aukuwar makamancinsa a Karim Lamido.

Daga nan, ya yi ta’aziyya ga ‘yan uwan waɗanda suka mutu a hatsarin, tare da yin addu’a ga marigayan.

Ya kuma ce an fara bincike domin gano dalilin aukuwar wannan hatsari da ma wanda ya faru a baya kwanan nan.

By Editor