WAEC za ta fara amfani da tsarin rubuta jarrabawa na ‘CBT’

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC), ta bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za ta fara amfani da tsarin rubuta jarraba ta yin amfani da kwamfuta wanda aka fi sani da CBT a taƙaice, ga ɗalibai masu zaman kansu da za su yi rijista a ƙarƙashinta.

Sanarwar da sashen hulɗa da jama’a na WAEC ya fitar mai ɗauke da sa-hannun babban jami’in hukumar, Moyosola F. Adesina a Yaba, Legas, ta ce ya zuwa ranar Litinin, 18 ga Disamban 2023 za ta fara yi wa mabuƙata rijista.

Sanarwar ta nuna hukumar za ta fara amfani da tsarin rubuta jarrabawa na CBT ne domin tafiya daidai da zamani.

Don haka ta sanar da al’umma da masu ruwa da tsaki cewa ta kamnmala tsare-tsare domin fara rubuta jarrabawar WASSCE ga masu zaman kansu a maimakon tsarin amfani da takarda da fensir da aka saba gani.

“Sabon tsarin zai fara aiki ne da ɗalibai masu zaman kansu waɗanda za su rubuta jarrabawar WASSCE a 2024 wadda za ta kankama a watan Fabrairun shekarar,” in ji sanarwar.

By Editor