Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
A kullum manazarta da masana al’amuran yau da kullum za ka ji hikimomi a lafuzansu, kamar da suke cewa, “mai uwa a gindin murhu…”, suka ce, “ba zai ci tuwansa gaya ba,” wato ba miya. Amma abin takaici a Nijeriya da muke da rijiyoyin man fetur sama da 100 da suke fitar da ɗanyen man fetur fiye da ganga milliyan biyu a kullum, amma matatun man fetur na ƙasa ba sa aiki sama da shekaru 10, kuma babu wani dalili tartibun na rashin aikin nasu.
Idan muka bi tarihin kakkafa matatun makamashin man fetur da dangoginsa a Afrika an fara ne a shekara ta 1954 a Algies, inda aka yi haxin gwiwa tsakanin CFP da kamfanin Total, daga nan sai a birnin Durban na Afrika ta Kudu, shi ma haxin gwiwa da kamfanin qasa da ake kira Socony da kuma Kamfanin Mobil. Daga nan sai ƙasashen Afrika suka ƙarfafi wannan sana’a ta tace man fetur da dangoginsa. Daga shekara ta 1958 zuwa 1963 ƙasashe irin su Luanda da Kenya da Ghana da Senegal, amma hakan bai yiwu ba sai da haɗin gwiwa da kamfanonin ƙasashen waje irin su Shell da BP da Total da Agip da ENL da kuma Kamfanin Consortium na Faransa.
Ita kuwa wannan ƙasa ta Nijeriya ta fara tace man fetur a shekara ta 1965 a ƙauyen Alesa Eleme a kusa da birnin Fatakwal (Port Harcourt), inda ake tace sama da ganga a 38,000 a kullum, wanda a lokacin ya isa ƙasa bakiɗaya har da rara. Yayin da buƙata ta ƙaru, saboda yawan jama’a masu ababen abun hawa daga kekuna zuwa babura da motocin hawa da na haya da na ɗaukar kaya nan da nan Nijeriya ta buɗe matata ta biyu a garin Warri a shekara ta 1978, inda take tace ganga sama da 125,000 a kullum.
A shekara ta 1980 lokacin da Nijeriya ta shige gaba wajen fitar da ɗanyen man fetur da dangoginsa zuwa ƙasashen waje, kuɗaɗe suna shigowa Nijeriya ko ta ina, inda aka shiga bushasha da kuma kece raini a tsakanin al’umma, aka shiga gasar sayen ababan hawa, inda za ka tarar mutum ɗaya yana da motocin hawa biyu-uku baya ga ta zuwa unguwa da kuma motar zuwa ‘shopping’ da ta yara. Wannan ya tilasta wa gwamnati ta sake buɗe wata matatar a garin Kaduna da kuma guraren ajiyar man fetur a Kano da Katsina da Sokoto da Gusau da Maiduguri da kuma Tola Adamawa, domin a sami sauƙin rarrabawa ga ‘yan ƙasa.
Matsalolin matatun man fetur da kuma dangoginsa a Afrika, musamman a cikin gida Nijeriya duk da tanade-tanade da hukumomi da ƙwararru suke yi, amma kullum abubuwa sai taɓarɓarewa suke yi, kamar ciwon Bamaguje – babu “sauqi”, inda dagaa matsaloli 81 da aka gano kashi 53 daga cikin 100, dukkansu sun samo asali ne daga lalacewar injina waɗanda ake cewa “Mechnical Outages”. Kashi 47 cikin 100 su kuma sun samo asali da sace-sace da wasoso da ɓarnar dukiyar ƙasa babu gaira babu dalili, inda ma’aikatan hukuma suke arzirta kansu da dukiyar ƙasa son ransu.
Tun daga shekara ta 1995, ‘yan Nijeriya suke haɗa baki da takwarorinsu masu wannan sana’ar man fetur na ƙasashen waje; Shell da BP da Total da Agip da EXXON Mobil da Chevron da kuma shi kamfanin qasa (NNPC) da su kansu ‘yan kuci-ku-bamu irinsu II Plc, Conoil Plc, Ardova Plc, MRS Oil Nigeria Plc, OVH Energy Marketing Limited da kuma Total Nigeria Plc. Waɗannan da suka haɗa kansu a shekara ta 2001, domin yaƙar duk wani mahaluki da zai kawo musu cikas wajen sharɓar alfanu daga wannan dukiya ta ƙasa.
A watan Agusta na shekara ta 2006 suka tabbatar wa kansu cewa babu wani mahaluki da Allah ya halitta a cikin gida Nijeriya ko a waje da ya isa ya hana su cin moriyar wannan dukiya ta wannan makamashi – man fetur da gas – kowanne iri ne a doron ƙasa (downstream).
A watan Disamba na shekara ta 2022, NNPC ya tabbatar da cewa, kamfanoni 20 ta yarda da su wajen gudanar da hulɗa da su. Waɗannan kamfanoni 20 suna kashe sama da Naira Biliyan 34.44 a duk wata shida ga ma’aikatansu a albashinsu. Wannan ya yi nuni da irin ƙarfinsu cikin ƙasa.
Saboda haka hana su ‘subsidy’ – tallafi a wannan harkar sai jarimin gaske, domin kuwa za su yi duk wata hanya da za ta karya ka, kuma za su saye zukatun talakawa ta yin farfaganda ta zahiri ta sanya tsoro da yunwa da firgici da tsadar kayan masarufi da kuma rashin kuɗi a hannun jama’a, kamar yadda muke gani a yanzu.
Wannan ƙungiya ta MOMAN ta fi ƙarfin kowa a Nijeriya, sai dai a yi mata taron dangi na talakawa da gwamnati, wato al’ummar ƙasa su cure guri guda su ba wa shugabanni da suka zaɓa, kamar Shugaba Chief Bola Ahmed Adekunle Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima Mustapha – ta yi musu biyayya ta haƙiƙa, su kuma su yi musu adalci tsakaninsu da Allah.
Sauran jam’iyyu irin su PDP da LP da APGA da NNPP da kuma sauran ƙananan jam’iyyu na dawa su ma wajibi ne a gare su, su bayar da goyen baya wajen yaƙar manufofin waɗancan ƙungiyoyi har da su ’yan ƙasa – wato MOMAN, domin cimma nasara wajen dawo da arzikin ƙasa ga ’yan ƙasa. Haka ƙungiyoyin ma’aikata su ma wajibi ne a gare su, su bayar da haɗin kai, domin a cimma buri.
Waɗannan kamfanoni masu kasuwancin makamashi kowanne iri har da shi man fetur da gas da sauran ma’adanai a duk faɗin duniya su ake kira ‘Multinational’. Wato komai da ruwansu, suke tafiyar da Bankin Duniya da Hukumar Lamini ta Duniya – IMF da kuma Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, da sauran hakumomi da suke da alaƙa da tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma.
Dole ƙasa kamar Nijeriya da takwarorinsu irin Marokko da Aljeriya da Libya da Misira (Egypt) da Sudan ta Arewa da ta Kudu da Kenya Afrika ta Kudu da Angola da Ghana – su koyi ɗabi’ar mun-ƙi.
Shawara tartibiya ita ce, raba auren zobe da aka yi da Nijeriya da qasar Birtaniya a shekara ta 1960, kuma ’ya’ya da aka samu cikin wannan aure, mu ba su zavi na ina za su koma da zama – Birtaniya ko maqotanta, wato Faransa ko Potugal ko Jamus – kai, kowacce ƙasa ta Yammacin Turai duk ɗaya ne, babu mu babu su, ko da kuwa ziyara ce ta ’yan uwantaka mun gode, Allah ya raka taki gona.
Saboda haka a sauya tsarin ilimi da kiwon lafiya da tsarin tattalin arziki da siyasa, wato mu soke tsarin mulkin dimukraɗiyya irin na Amurka, wato tsarin bariki, wato tsarin kazo-nazo, babu ruwan kowa da kowa, kowa ta sa ta fishhe shi, inda amana da gaskiya da jajircewa ba sa aiki – sai ƙarya da yaudara da kuma manufarci su ne ababan kama shugaba mai gaskiya da amana da kuma tausayawa na ƙasa.
Duk wani tsari idan daga Majalasar Ɗinkin Duniya yake tsari ne na Amurka da ‘yan kanzaginta, musamman Birtaniya da Faransa – sai ‘yan kaɗan da su ma a yanzu ta kansu suke yi.
Saboda lokaci za mu taƙaita sai mako mai zuwa mu yi kira da Nijeriya da ta jagoranci bore, kamar yadda Rasha ta jagoranci kafa ‘BRICS”. Saboda haka idan Allah ya kai mu mako mai zuwa, za mu feɗe biri har bindinsa dangane da wannan ƙunkiya ta BRICS.
