Jihohin Katsina, Zamfara, Borno, Kano, Kaduna, Yobe, Nasarawa da Katsina kusan mutane miliyan 20 suna fuskantar qarancin abinci saboda janye tallafin mai da gwamnatin da ta gabata ta assasa sabuwar gwamnatin Tinubu kuma ta aiwatar. Lamarin ya sa mutane ba sa iya sayen abinci su ci saboda matsanancin talauci da rashin tsaro ya haifar.
Dokta Abubakar Sulaiman mataimakin shugaban hukumar samar da abinci da bunƙasa noma na Majalisar Ɗinkin duniya shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da BBC. Inda ya ce, janye tallafin mai ya sa matuƙar ana son mutane su rayu dole a ba su kuɗin sayen abinci ko abinci tare da bunaasa nomar rani Arewacin Nijeriya da kiwon lafiya kyauta.
Tun daga lokacin janye tallafin Mai kusan Kashi 70 cikin ɗari na ‘yan Nijeriya sana’a da albashi basa iya ciyar da mutane. Hatta masu noman rani a bana akasari sun ce ba za su iya aiki ba saboda tsadar mai.
Kamfanoni suna ta rufewa saboda tsadar fetur da gas da rugurgujewar naira da tsadar dala ko ƙarancin ta. Haka ‘yan kasuwa manya da ƙanana sunata karyewa saboda ribar da suke samu bata iya ciyar da su har sun kai ga cinye uwar kudu, wasu har basukan abokan hulɗa ya sa sun sayar da shaguna ko gidajen kwana don warware matsala wasu kuma har sun dangana da gidajen yari.
A daidai lokacin da ake fuskantar wannan masifar yadda rashin tsaro da yunwa ke salwantar da rayukan mutane, shugaban ƙasa Bola Tinubu lokacin ke neman majalisa ta ba shi damar sayo jirgin ruwan shaƙatawa a teku na naira milyan dubu biyar da Motocin alfarma na naira bilyan dubu biyu da rabi da motocin matarsa na naira bilyan dubu biyu da gyara gidansa a kusan naira bilyan dubu biyar. Tuni su ya majalisar tarayya kusa 500 aka saya wa kowa motar naira milyan 160.
Daga Muazu Harɗawa Edita Jaridar Alheri Bauchi. 08062333065.
