22
Jun
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jam'iyyar ADC mai alamar musabaha reshen jihar Kano, ta gudanar da taron gangamin na ƙoƙarin haɗa kan jam'iyyu domin yanda za a haɗu domin a tunkari kawar da jam'iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Taron ya sami halartar dukkanin musu ruwa da tsakin jam'iyyar ADC na jihar da wakilan wasu jam'iyu da suka haɗa da PDP da PRP da sauran wasu jam'iyyun da kuma wasu malaman jamia da suka gabatar da jawabai akan abinda ya shafi haɗin kai. A yayin taron daya gudana a ɗakin taro na Mumbayya tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kano…
