2027: Masu sauya sheƙa zuwa APC masu zunubi ne da ke neman gafara – Dalung

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana ‘yan siyasa da ke sauya sheƙa daga jam’iyyun hamayya zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matsayin masu zunubi da ke neman gafara.

Dalung, yayin da ya ke jawabi a Abuja, ya musanta ra’ayin da ke cewa ‘yan siyasa na komawa APC ne saboda jam’iyyar ta tabuka abin a zo a gani. A cewarsa, “a’a, masu zunubi ne da ke neman gafara daga zunubansu da dama.”

Dalung ya ce masu sauya sheƙar suna kawai cika abin da tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya taɓa faɗi dangane da ‘yan siyasar da suka yi almundahana, cewa duk girman zunubansu, da zarar sun shiga APC, ana gafarta musu.

Ko da yake Oshiomhole ya musanta wannan magana a lokuta da dama, amma ‘yan siyasa na ci gaba da amfani da ita.

Ya ce: “Waɗannan mutanen sun aikata manyan laifuka masu muni ga al’ummar Nijeriya, kuma yanzu suna tsalle zuwa cikin jirgin APC don a gafarta musu. Ba wai suna goyon bayan Tinubu ba ne – a’a, ba sa goyon bayansa. Suna taruwa ne kawai don a gafarta musu.”

By ukarofi