Sharhin fim ɗin ‘Da Na Sani’

Spread the love

Daga HABIBU MA’ARUF ABDU

Kamfani: Kannywood Movie Hub

Labari/Tsarawa: Yakubu M. Kumo

Shiryawa: Amina Adam Yusuf

Darakta: Bifa Mohammed Adamu

Yan wasa: Aminu Shariff (Momo), Amina Lulu, Tahir Ibrahim Tahir, Saddiƙu Artist, Mustapha Musty.

Bayan bullowar finafinan Hausa masu dogon zango (Series films), ‘yan kallo da dama sun shiga kewar gajerun finafinai (feature length films). Da yawa daga cikin ‘yan kallo basa iya bibiyar finafinan masu dogon zango daga farko har zuwa ƙarshe. Haka kuma, tsawaita labaransu kan haifar da karancin nishaɗi a wasu lokutan. Wannan yasa yan kallo suka daina samun armashi da gamsuwar kallon fim daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda suka saba a baya, har takai ga wasu sun daina bibiyar finafinan na Hausa gabaɗaya.

To yanzu dai, alhamdulillah, gajerun finafinan sun fara dawowa. ɗaya daga cikin manyan jajirtattun da suka taka rawa wajen dawo dasu shi ne producer Abdul Amart (Mai Kwashewa), wanda ya haɗa hannu da Kannywood Moɓie Hub wajen ƙirƙirar ‘Taskar Kannywood’, inda suke fitar da fim guda mai cikakken labari duk ranar Lahadi.

Duk da cewa an ɗauki sati 6 ana gabatar da finafinai mabanbanta a Taskar Kannywood, hankalin mutane bai karkata kansa ba sai bayan da suka fitar da fim na bakwai, mai suna ‘Da Na Sani’. Wannan fim ya ja hankalin mutane sosai wanda yanzu haka yana ta yawo a kafofin sada zumunta.

‘Da Na Sani’ fim ne mai cike da ma’ana, nishaɗi, da motsa zuciya. Labarine na wasu sabbin ma’aurata; Mansur (Aminu Sharif Momo) da matarsa Samira (Amina Lulu). Samira yarinya ce mai shekaru 18, wadda take ɗabi’un kuruciya saboda ƙarancin shekarunta. Ta kan toshe kunnuwanta da earphones tana sauraron waƙoƙi, tana danna waya, ko wasa da game a koda yaushe.

Duk da cewa tana nuna ƙauna da ƙoƙari wajen farantawa mijinta Mansur rai, shi bai fahimci haka ba. Ta kan yi masa wasan soyayya ta hanyar tsokana kamar ɓoye mukullan motarsa ko tsoratar da shi da wasa, amma shi sai ya ɗauki hakan a matsayin rashin kunya da kuma wasa da aure.

Wata rana Mansur yana cikin bacci sai Samira ta yi masa zane a fuska, ta rubuta kalmomin soyayya irin su “I loɓe you” tare da zanen Heart. Da ya farka ya shiga banɗaki ya ga zanen, sai ya fusata, ya mammareta, ya kuma gargaɗe ta da kada ta sake yi masa irin wannan.

Wannan abu ya girgiza Samira sosai, domin ita tayi zaton mijinta zai zama irin mazan cikin labaran littafai “mijin noɓel”, abokin wasa, mai fahimta da raha. Amma sai gashi yau ya mare ta saboda abin da ita take gani a matsayin soyayya.

Bayan an yi rikicin, ta bashi haƙuri, shi kuma ya fice daga gida. Ya haɗu da abokinsa (Tahir I. Tahir), wanda yai masa nasiha, ya ce masa irin abubuwan da Samira ke yi alamar ƙauna ne, ba raini ba. Mansur ya gane gaskiya, sai ya nufi gida don sulhu, har ma ya biya shopping ya siyo mata Ice Cream da Chocolates.

Abin mamaki, bai tarar da ita a gida ba. Daga nan ne aka kira shi daga asibiti, tuni zuciyar Samira ta buga. Lokacin da ya je asibitin kuma mai afkuwa ta riga ta afku; Samira ta rigamu gidan gaskiya. 

Fim ɗin ya ƙare da ban tausayi lokacin da Mansur ya dawo gida ya tarar da wasiƙa wadda Samira ta bar masa, inda ta bayyana cewa duk abin da take yi, don ƙauna da fatan canza shi zuwa mutum mai sakin fuska ne, ba don raini ba.

‘Da Na Sani’ fim ne da ya haɗu sosai kuma yake cike da darasi, motsa zuciya da faɗakarwa. Amma da ace an ƙara inganta labarin ya ɗan fi haka tsayi, kuma an tsarashi don nunawa a sinima, da sai ya fi haka tasiri kuma ya fi zama gagarabadau.

Fim ɗin ya yi nuni da yadda rashin fahimtar juna da saurin fushi ke iya jawo hasarar abubuwa masu daraja a rayuwa. Ya kuma nuna yadda ƙauna da yawan soyayya suke iya tafiya a banza idan ba a samu daidaiton ra’ayi tsakanin ma’aurata ba. Mazaje da yawa suna neman matar aure irin Samira, amma shi Mansur gashi ya samu amma bai san muhimmancin haka ba saboda tsatstsauran ra’ayinsa.

Ma’aikatan fim ɗin, daga kan marubuci, darakta, producer, da jarumai duka sun cancanci yabo. Marubuci ya rubuta labari mai kyau, amma kyakkyawan aikin darakta da ‘yan wasa su ne suka busawa labarin rai har ya ɗauki hankali yadda ya kamata. Dama shi Aminu Shariff Momoh an sanshi wajen taka kyakkyawar rawa a finafinan zamantakewar aure. Jaruma Amina Shehu ita ce ta bada mamaki irin ƙoƙarin da ta yi duk da cewa ba wata jarumace shahararriya ba. Ta bayyana kwarewarta kuma nasan kwanannan frodusoshi za su yi caa a kanta.

A taƙaice, fim ɗin ‘Da Na Sani’ ya cika dukkan sharuɗɗan kayatarwa da faɗakarwa — da kyakkyawan rubutun labari, kyakkyawar taka rawar ‘yan wasa, ma’ana da ƙarfin darasi. Ina bada shawarar kowane mai sha’awar fina-finan Hausa, musamman waɗanda ke neman labari mai motsa zuciya da darasi, su kalli wannan fim.

By ukarofi