Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayayyakin noma ga magidanta 1,000 da suka haɗa da ‘yan gudun hijira daga Mandunari da ke ƙaramar Hukumar Gujba da sauran al’ummomin da suke zaune a yankin.

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Damaturu, Buni ya bayyana cewa, duk da cewa al’ummomin Mandunari ya kasance su ne yankin al’umma guda ɗaya tilo a jihar Yobe da har yanzu ba a sake tsugunar da su ba, al’ummarta sun nuna jajircewarsu na komawa gidajen kakanninsu.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na tabbatar da dawowar duk ‘yan gudun hijira lafiya, tare da tallafa musu  ta hanyar saka hannun jari a ayyukan more rayuwa, tsaro, gidaje, kiwon lafiya, da ilimi.

Kayayyakin da aka bada tallafi ga manoman sun haɗa da ingantattun kayayyakin yin noma da irin masara, kuɓewa, gyaɗa, gero, da irin shinkafa, taki, maganin kashe ƙwari da na ciyawa da makamantansu.

“A lokacin rani, manoma za su samu famfunan ruwa da ingantattun irin albasa, tumatir, kabeji, latas, da barkono.

“Gwamnatin jihar Yobe ta riga ta zuba jarin sama da dala biliyan 4 a ayyukan noma a faɗin al’ummomi 178 na mazabun Jihar, inda ta samar da taraktoci, takin zamani, da sauran kayan masarufi don bunkasa samar da abinci,” inji gwamnan.

Ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar hukumar raya ƙasa da haɗin gwiwar ƙasar Switzerland za ta tallafa wa ƙarin magidanta 2,000 da kayan noma da kiwo a Gaidam, Tarmuwa, da Damaturu.

Buni ya ƙara da cewa, ƙananan manoma za su kuma samu horo kan noma da kiwo da sauyin yanayi, yayin da a ƙarƙashin shirin samar da mafita mai ɗorewa manoma 1,000 da ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta horas da su za su samu kananan tallafi don ci gaba da rayuwarsu.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a bar wata al’umma a baya ba, duk wanda ya rasa matsugunai ya cancanci a ba shi dama mai kyau don sake gina rayuwarsu cikin aminci da mutunci,” inji gwamnan.

By ukarofi