Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Fansho ta ƙasa (PenCom) tana aiki tare da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (OHCSF) don ɓullo da shirin bayar da tallafi na shekara-shekara na Naira Biliyan 30 ga ma’aikatan da ke ritaya a ƙarƙashin shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS).
Omolola Oloworaran, Darakta Janar na PenCom ne ta bayyana haka a lokacin wata ziyarar ban girma da ta kai wa Didi Esther Walson-Jack, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya a Abuja, domin tattaunawa kan yadda ake gudanar da sauye-sauyen fansho da kuma shirye-shiryen inganta jin daɗin ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Oloworaran ta bayyana cewa PenCom tana kammala hanyoyin da za a kafa tsari ga ma’aikata da ke samun tallafi bisa ga sashe na 4 (4) (a) na Dokar Gyaran Fansho (PRA) 2014.
Ta ce shirin da aka tsara zai samar da biyan kuɗaɗen lokaci guda a lokacin ritaya, baya ga haƙƙin fansho da ake da su a ƙarƙashin CPS.
A cewar Shugabar PenCom, shirin, idan aka saita kashi 100 cikin 100 na babban albashin shekara-shekara na mai ritaya, zai jawowa gwamnatin tarayya kashe kimanin naira biliyan 30 a duk shekara. Wannan adadin, inji ta, an saka hannun jari ne mai sauƙi amma mai tasiri wajen girmama hidima da sadaukar da kai na ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Oloworaran ta kuma nuna damuwarta kan yadda ake ci gaba da samun jinkirin biyan kuɗaɗen fansho.
Ta bayyana nasarorin da aka samu a baya tsakanin PenCom da OHCSF, wanda ya sa Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da bayar da lamuni na biliyan N758 don kawar da wasu manyan lamunin fansho.
