Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanata mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta yamma, Ahmed Wadada, ya bayyana shirinsa na ficewa daga jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, zuwa jam’iyyar APC.
Wadada ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a garin Keffi na jihar Nasarawa a ranar Asabar.
A cewarsa, sauya sheka da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi zuwa SDP na daga cikin manyan dalilan da suka sa ya yanke wannan shawarar.
Ya ce ba zai iya zama jam’iyya da El-Rufai ba saboda bambancin akida ta siyasa.
“Duk da cewa Malam El-Rufai yayana ne, amma ba na jin zan iya zama da shi a jam’iyyar SDP saboda shi ba dan siyasa ba ne,” in ji Wadada.
Ya yi mamakin dalilin da yasa El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC da kuma barin shugaban kasa Bola Tinubu bayan ya yi kakkausar suka kan sauya mulki zuwa Kudu.
