Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Shekaru 26 da kafuwar tsarin mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya ba tare da katsewa ba, abin alfahari ne ga kowanne ɗan ƙasa, saboda ko ba komai ’yan Nijeriya suna rayuwa cikin ’yanci da walwala ba tare da ƙuntatawa da danniya irin ta mulkin soja ba. Kamar yadda muka sani shi tsarin shugabanci irin na dimukraɗiyya tsari ne da ke nufin gwamnatin jama’a wacce jama’a ke yankewa kansu shawara kan wanda zai wakilce su ko kuma ya shugabance su. Wannan wani tsari ne da jama’a ke da ‘yanci ta fuskar siyasa wanda ya dogara kan tsarin gudanar da zaɓe bisa gaskiya da ’yanci, ba tare da nuna wariya ko bambanci ba.
A cikin tsawon shekaru 26 da suka shige Nijeriya ta kasance cikin mulkin dimukraɗiyya, abinda ake ganin gagarumin cigaba ne domin shi ne lokaci mafi tsawo da aka samu mulkin farar hula tun bayan da samun ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1960 ba tare da juyin mulki ba. Daga shekarar 1999 da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya karɓi ragamar jagorancin mulkin Nijeriya, wanda ya taɓa riƙe shugabancin ƙasar a ƙarƙashin mulkin soja, an yi jerin shugabanni guda huɗu, da suka haɗa da marigayi Umaru Musa ’Yar’adua, Goodluck Ebele Jonathan, Muhammadu Buhari da kuma shugaban ƙasa na yanzu Bola Ahmed Tinubu.
Ranar Dimukraɗiyya ta ƙasa wacce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo da ita zuwa ranar 12 ga watan Yuni a shekarar 2018, a maimakon ranar 29 ga watan Mayu, wanda a baya ake bikin, da a yanzu take matsayin ranar miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati, domin tunawa da zaɓen shugaban ƙasa na 1993, wanda marigayi Moshood Abiola ya lashe a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, amma gwamnatin mulkin soja da Ibrahim Badamasi Babangida ke jagoranta ta soke.
Tun bayan kafuwar mulkin dimukraɗiyya, an samu sauye-sauye da dama a Nijeriya, musamman kan sha’anin gudanar da zaɓe, rijistar jam’iyyun siyasa masu yawa, hukunce-hukuncen kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe, ayyukan raya, da naɗe-naɗe a muƙamai daban-daban. Kowanne ɓangare daga cikin shiyyoyin mulki na ƙasar nan ya samu wakilci a Gwamnatin Tarayya, an yi zaɓen ’yan majalisar ƙasa da na jihohi. An kafa sabbin dokoki waɗanda a baya babu su, kamar dokar ‘yancin cin gashin ƙananan hukumomi, da ɓangaren shari’a. Gwamnati ta ƙara matsawa kusa da talakawa, jama’a na cigaba da gogewa da tsarin siyasa, suna daɗa wayewa da sanin ‘yancin kansu, da ’yancin faɗin albarkacin bakin su.
Wani babban abinda ke bambanta mulkin soji da na farar hula shi ne wanzuwar majalisun dokoki. A tsarin dimukraɗiyya dai haƙƙin majalisun dokokin ne su kafa sabbin dokoki; su gyara waɗanda ba a gamsu da su ba; su kuma sa’ido ga abubuwan da jami’an gwamnati ke yi, don tabbatar da ganin cewa ba a ci amanar jama’a ba.
Kamar yadda masu hikimar magana ke cewa, Siyasa Rigar ‘Yanci, babu shakka ‘yan Nijeriya sun samu nasarori masu yawa wajen samun damarmaki, wanda ya basu zarafin samun romon siyasa, a ƙarƙashin tsarin mulkin dimukraɗiyya. An samu muƙamai da ayyukan yi. ‘Yan Arewa da dama sun samu manyan muƙamai a lokacin shugabancin ɗan Arewa, Muhammadu Buhari, kamar yadda a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ’yan yankin Kudu suka mori muƙamai masu maiƙo. Haka ma yanzu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ya fito daga yankin gabashin ƙasar nan, ana damawa da ’yan ƙabilarsa ta yarabawa sosai, sakamakon manyan naɗe-naɗe da ake yi musu. Duk kuwa da kasancewar basu ba da wata gudunmawar a zo a gani ba lokacin yaƙin neman zaɓe da gwagwarmayar kafuwar gwamnatinsa.
Manazarta harkokin siyasa na ganin irin wannan hali na nuna wariya wajen ba da muƙamai ko samar da ayyukan yi a Nijeriya na haifar da komabaya ga cigaban siyasar ƙasar nan. Bayan ƙalubalen da cin hanci ne da rashawa ke haifarwa. Tsarin na dimukraɗiyya dake matsayin tsari mai manufa ta baiɗaya, a ko’ina a duniya, amma a nan ƙasar yadda muke aiwatar da shi ya saɓawa yadda ‘yan siyasa da mahukunta ke ganinsa.
Wani ƙalubale kuma da dimukraɗiyyar ƙasar nan ke fuskanta shi ne halayyar nuna danniya da manyan jam’iyyun siyasa ke nuna wa ƙanana, da kuma yunƙurin mayar da ƙasar ƙarƙashin mulkin jam’iyya ɗaya. Mun ga yadda jam’iyya mai mulki ke cigaba da zawarcin manyan ’yan siyasa, da ƙungiyoyin jama’a daga kowanne ɓangare na ƙasar nan. Yayin da wasu ke barin ƙananan jam’iyyun da aka zaɓe su ko suke da rijista zuwa jam’iyya mai mulki ta gwamnati, don kwaɗayin samun muƙamai da romon dimukraɗiyya. Babu shakka hakan na da haɗari sosai a tsarin dimukraɗiyya, don yana hana ’yan adawa bakin magana, da karya lagonsu a siyasance. Alhalin ita dimukraɗiyya ba ta armashi in babu ’yan adawa masu ƙarfin faɗa a ji, waɗanda za su riƙa zaburar da gwamnati. Sannan samun jam’iyyu masu yawa a siyasa su ne adon dimukraɗiyya.
Idan kuma aka waiwayi ɓangaren tattalin arziki, talakawan Nijeriya na fuskantar ƙalubale masu yawa, sakamakon canje-canje gƙame da tsare-tsaren tattalin arziki da sabbin dokokin haraji da suka sa talakawa cikin ƙuncin rayuwa, saboda tsadar kayayyakin masarufi da sauran harkokin gudanar da rayuwa. Har an samu wasu da ke ganin da irin dimukraɗiyyar da ake yi yanzu gara ma a koma mulkin soja, ko za a samu sassauci. Kodayake, gwamnatocin da ake ganin su ne da alhakin kawo wahalhalun rayuwa ga ‘yan Nijeriya, su ma suna bayyana ƙoƙarin da suke yi na ganin an kyautata al’amura. Yayin da rahotanni ke bayyana nasarori da ake samu game da kimar da Nijeriya ke samu a idon duniya, sakamakon irin matakan da gwamnati ke ɗauka na farfaɗo da tattalin arziki, bunƙasa ayyukan gona, da samar da ayyukan yi ga mata da matasa.
Akwai wasu ’yan Nijeriya dake ganin duk da cewa an shafe shekaru ashirin da shida kan turbar dimukraɗiyya, rashin kyakkyawan shugabanci shi ne ummul-haba’isin matsalolin da ake fuskanta. Amma yadda wasu ’yan siyasa da shugabanni ke yin karan-tsaye ga tanade-tanaden tsarin na dimukraɗiyya, wajen murɗiyar zaɓe, almundahana da dukiyar ƙasa, da ɗauki ɗora ba tare da amincewar ’yan ƙasa ba, suna kawo cikas ga cigaban da ake burin gani, abinda shugabannin ke musantawa.
Daga cikin hanyoyin da za a bi domin gyara siyasa da dimukraɗiyya a ƙasar nan, akwai baƙatar kawo ƙarshen siyasar ubangida, da siyasar ƙabilanci, ko sanya addini a wajen zaɓen ɗan takara, kamar yadda muka gani a zaɓukan baya. A gaskiya siyasarmu ba za ta taɓa ci gaba ba, saboda yadda masu mulki ke fifita iyayen gida a maimakon talakawa. Ko kuma fifita ’yan ƙabilarsu ko addininsu, wajen rabon muƙamai, kamar yadda na yi bayani a baya.
Sannan harwayau, akwai buƙatar kawar da batun zaɓen fitar da ’yan takara na wakilan jam’iyya, wato zaɓen deliget, wanda a baya ya kawo ruɗani da hargitsi a matakin fitar da ‘yan takarar da za su wakilci jam’iyyunsu a babban zaɓe. Wannan tsari na deliget tsari ne da ke cike da rashin gaskiya da cin hanci da rashawa, inda sai ɗan takara mai ƙumbar susa ko wanda yake da babban ubangida, da wanda gwamnati ke goyawa baya ne kaɗai suke samun nasara, koda kuwa ’yan jam’iyya na so ko basa so.
Akwai batun rashin cika alƙawarin ’yan siyasa, da yadda wasu ke nisantar talakawan da suka zaɓe su ko rashin jajircewa don ganin an yi musu ayyukan raya ƙasa, daga kasafin kuɗin gwamnatin tarayya da na jihohi. Wasu ’yan siyasar ba sa waiwayar talakawansu, sai sun ga lokacin zaɓe ya gabato. Alhalin sun bar talakawan su cikin yunwa da talauci, da rashin tsaro, rashin ilimi, da rashin ingantattun cibiyoyin kula da lafiya, da rashin ruwan sha da wutar lantarki. A taƙaice dai babu ribar dimukraɗiyya, sai dai talakawa su riƙa ji a rediya an ware miliyoyin kuɗi don ayyukan raya ƙasa, amma ba sa gani a ƙasa.
