Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba zaɓen 2027 ba — ACF

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027.

ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin da ƙungiyar ke cewa hakan ya yi wuri.

Wannan kira dai na kunshe cikin wata sanarwar yi wa musulmi barka da Sallah Babba da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar.

ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da tsadar rayuwa da rashin wutar lantarki da matsalolin lafiya, ilimi da karyewar darajar Naira da tashin farashin kayan abinci.

ƙungiyar ta kuma nuna takaicinta yadda duk da irin waɗannan ƙalubale amma jam’iyyar APC ta fi mayar da hankali kan gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubun a 2027.

Ana iya tuna cewa a watan da ya gabata ne dukkanin gwamnonin jam’iyyar APC 22 a faɗin ƙasar suka amince da cewa Bola Tinubu ne ɗan takararsu a zaɓen 2027 mai zuwa, lamarin da ake ci gaba cece-kuce a kai.

By ukarofi