08
Jun
Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Shugaban ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF), Alhaji Yerima Shettima, ya yi martani dangane da kalaman da tsohon Gwamnan jihar Kaduna El-Rufa’i da tsohon Minista Rotimi Amaechi suka yi a taron da suka yi a Abuja, inda ya bayyana kalaman nasu a matsayin soki burutsu. Yerima Shettima ya ƙara da cewar a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin farfaɗowa daga matsalolin da suka addabe ta ɓangaren tsaro da tattalin arziki, abin takaici ne a samu irin waɗannan kalamai marasa kan gado na fita daga bakin waɗanda ake yi musu kallon manya. Ya ƙara da cewar…
