Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ƙarƙashin jagorancin Wole Adesina ta bayyana da kakkausar murya cewa jam’iyyar ba ta sayarwa ba ce kuma ba ta haya ba ce ga wani ƙawance ko motsi na siyasa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Barista Alfa Mohammed, ya jaddada cewa ba za a yi amfani da jam’iyyar SDP a matsayin wata kafa ta ƙaddamar da hare-hare kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba ko kuma inganta duk wani ƙawancen da ba shi da wata manufa mai inganci don kawo sauyi a Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kwamitin zartaswa na SDP na ƙasa ya bayyana a fili cewa jam’iyyar ba ta sayarwa ba ce ko ba da hayar wata ƙungiya, kuma ba za ta kasance cikin duk wani shiri na adawa da gwamnati ko kuma ƙawancen da ba shi da wata manufa ta sauya fasalin Nijeriya,” inji sanarwar.
Mohammed ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar ficewa daga duk wani ƙawancen da ta yi a baya, yana mai nuni da al’amuran da suka faru a shekarar 2019, lokacin da wasu gungun ‘ya’yan jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Farfesa Jerry Gana suka kutsa cikin jam’iyyar SDP tare da yunƙurin sace shugabanninta.
Mohammed ya ƙara da cewa, “Mun sha fama da wannan matsalar a baya, a shekarar 2019, wasu fusatattun da suka sauya sheƙa daga PDP suka bi mu suka yi ƙoƙarin ƙwace ragamar mulkin jam’iyyar, ba za mu bari tarihi ya maimaita kansa ba.
“Cin amanar shugabancin SDP ya haifar da murabus ɗin shugaban jam’iyyar na ƙasa a lokacin, Oba Olu Falae, wanda ya jefa jam’iyyar cikin rigimar shugabancin da ta kai ga ci gaba da gudanar da wasan wuta na shari’a.
“Yayin da sahihin kwamitin zartaswa na SDP na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Cif Adesina a yanzu ya zana halaccin kasancewarsa kai tsaye na Oba Olu Falae ya jagoranci kwamitin zartarwa na ƙasa da ya karɓi ‘yan PDP da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar, kashi na biyu, wanda Shehu Gabam ke jagoranta ya dogara ne kan rashin amincewar INEC da aka saya wanda ya ci gaba da fuskantar shari’a tun 2019.
“Daga sama, kwamitin zartaswa na SDP na ƙasa ya bayyana a fili cewa jam’iyyar ba ta sayarwa ba ce ko hayar wata ƙungiya, kuma ba za ta kasance cikin duk wani shiri na adawa da gwamnati ba da ba shi da wata manufa ta sauya fasalin Nijeriya.”
Mohammed ya ƙara da cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da tafiyar da gwamnati yadda ya kamata da kuma yi mata hisabi, amma ba za ta shiga cikin wata gamayyar ƙungiyoyi masu son kai da nufin kawo cikas ga gwamnatin zamanin da kuma hana ‘yan Nijeriya ribar ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.
Sanarwar ta yi kira ga shugabannin SDP a dukkan matakai da su bijirewa duk wani yunƙuri na ƙwace shugabancinsu tare da kai rahoto ga hukumomin da suka dace, tare da barin ƙofofin jam’iyyar a buɗe ga sabbin mambobin jam’iyyar na gaskiya.
Ya kuma yi kira ga ‘yan uwa da magoya bayansa da su kwantar da hankulansu tare da haƙuri, yana mai ba su tabbacin cewa, ana ƙoƙarin dawo da martabar hukumar zaɓe ta INEC ga halastaccen kwamitin zartaswa na ƙasa da suka zaɓa, kuma nan gaba kaɗan za a ba da cikakken bayani kan lamarin.
