25
May
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) reshen Jihar Gombe ta fito fili ta karyata ikirarin wani naɗin shugabanci bogi da ake dangantawa da ita, tare da gargadi kan wani taron sirri da ake zargin an shirya domin kawo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar. A wata sanarwa da Ambasada Injiniya M. Abdulkadir Kumo, mai ba da shawara na musamman kan harkokin watsa labarai ga shugaban jam’iyyar na jiha ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa ba ta taba amincewa da naɗin Dokta Sadiƙ Abubakar Gombe a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa (Arewa) ba, tana kira ga jama’a…
