PDP za ta zama gawa nan da ƙarshen 2025 – Ganduje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na kan hanyarta ta rushewa gaba ɗaya.

Ganduje ya mayar da martani ne ga kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda ya ce APC za ta watse nan ba da daɗewa ba, kuma tsofaffin ‘yan PDP da suka hada da Ganduje za su koma jam’iyyar adawa.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Lahadi, Ganduje ya bayyana wadannan kalaman da “marasa tushe kuma marasa ma’ana.”

Ya ce ba shi da wani dalilin barin APC zuwa abin da ya kira “jam’iyyar adawa mai gazawa.”

“A gaskiya ma, ba da daɗewa ba za mu karɓi Sule Lamido domin ba zai sami inda zai koma ba. PDP ta mutu,” inji shi.

Ganduje ya ƙara da cewa rabuwar kai da rikice-rikicen cikin gida da PDP ke fama da su za su haddasa rugujewarta kafin ƙarshen shekarar 2025.

By ukarofi