Ranar ma’aikata ta duniya: Shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Spread the love

Daga cikin hikima ta Ubangiji shi ne Ya sanya bambanci a tsakanin mutane; akwai mai kuɗi akwai talaka, akwai mai ilimi akwai jahili, akwai shugaba akwai mabiya, akwai ma’aikata akwai masu gidansu. Allah ya sanya wannan bambance-bambance domin wasu sashin suna ma wasu sashin hidima. Da babu bambanci nan da rayuwa ta ta’azzara kuma mutane sun ƙuntata. Da kowa mai kuɗi ne, da babu masu aikin ƙwadago, da babu manoma da za su shuka abinci da sauransu.

Ranar ɗaya ga watan Mayu, rana ce da Majalisar ɗinkin Duniya ta ware musamman domin yabawa ƙoƙarin da ma’aikata suke yi wajen kawo cigaba a cikin al’umma da kuma tattauna ƙalubalen da suke fuskanta a wuraren ayyukansu. Yana da kyau mu san waye ma’aikaci? Ma’aikaci shi ne mutumin da aka ɗauke shi wani aiki ko ƙwadago domin biyanshi ladan aikin in ya gama.

A Nijeriya, muna da nau’in ma’aikata guda biyu; akwai ma’aikata masu aikin kwadago da ke leburanci, ko aiki ƙarƙashin kamfanoni da ƙungiyoyi masu zaman kansu. Haka zalika akwai kuma ma’aikatan gwamnati.

Abin takaici ne kuma abin haushi irin zalunci da kuma tauye haƙƙin da ake yi wa ma’aikata a wannan ƙasar ta mu. Zaluncin ma’aikata ya zama ruwan dare a cikin al’umma. Wannan ya sanya da yawa daga cikin waɗannan ma’aikata suna fama da baƙin ciki da kuma ƙuncin rayuwa. Wasu suna zuwa wuraren aikinsu ne ba da son ransu ba, domin basu da wata damar ne. Daga cikin zaluncin da ma’aikata ke fuskanta akwai; rashin biyansu albashin su akan lokaci ko kuma rage wani kaso a cikin albashinsu ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. Akwai ƙarancin albashi, akwai kuma rashin wadata ma’aikata da kayan aiki na zamani. Haka zalika, akwai rashin horar da ma’aikata akan yanayin gudanar da aikin da zai dace da zamani, da kuma hana ma’aikaci samun girma a wajen aiki. Bugu da ƙari, akwai gajiyar da ma’aikata da aikin da ya fi ƙarfin su ko kuwa wahalar da su akan aikin da bashi wani amfani. Wasu ma’aikatan na fuskantar cin mutunci, da kuma wulaƙanci da zage-zage  a wurare aikinsu. Wasu kuma na fuskantar matsi na aikin alfasha, musamman mata.

Mun sani cewa bai wa ma’aikata kyakkyawar kulawa da kuma tausaya musu, na daga cikin kyawawan ɗabi’u. Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wa Sallama yana cewa, ‘Ma’aikatan ku ‘yan’uwanku ne. Ubangiji Ya sanya su a ƙarƙashin kulawar ku ne. Saboda haka, duk wanda ɗan uwansa yake ƙarƙashin kulawar sa; ya ciyar da shi da irin abinda shi zai ci; ya kuma tufatar da shi da irin nau’in tufafin da zai saka. Sa’annan kada ku kallafa musu aikin da ya fi ƙarfin su, ko wanda ba za su iya ba. Inda kuma baku da wata damar sai dai ku saka su aikin to, ku sauƙaƙa musu wajen ƙaddamar da ayyukan’.

Haka zalika, mu sani cewa biyan ma’aikata haƙƙoƙin su na albashi ko kuɗin alawus-alawus ɗin su, da kuɗaɗen su na sallama akan lokaci, na daga cikin kyawawan halayen da za su kawo wa ƙasa da kuma al’umma cigaba. Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wa Sallama yana cewa, ‘A bai wa mai ƙwadago haƙƙin sa kafin guminsa ya bushe’.

Harwayau, mu sani cewa rashin biyan ma’aikata haƙƙoƙin su ko albashin su na da mummunan tasiri akan su ma’aikatan, da kuma ma’aikatar da suke wa aiki, da ma al’ummar gari. Rashin biya wa ma’aikata albashin su yana janyo wa ma’aikaci rashin kuɗi wanda na iya hana su samar wa iyalansu abinci, kuɗin makaranta, kuɗin haya da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya. Wannan yanayin na iya jefa ma’aikaci a cikin ƙunci da wahalhalun rayuwa wanda ka iya kawo masu jinya a jiki ko kuwa a ƙwaƙwalwa. Bugu da kari, rashin biyan ma’aikata haƙƙoƙin su na haifar da ruhin neman kuɗin gaggawa ta kowacce hanya. Wannan na iya ɗora su a hanyoyin da ba su dace ba, wajen neman dukiya kamar sace-sace, damfara, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da sauran su. Hakan na iya ƙara ayyukan ta’addanci a ciki gari.

Matsalar da ma’aikata za su fuskanta wajen rashin biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu na iya rage masu ƙarfin gwiwa wajen aikinsu. Idan ma’aikaci yana fuskantar rashin kuɗi ko kuwa yana shakka ko za a biyan shi ko kuwa a’a yakan saka shi yayi ko oho da aiki. Da kuma ƙin kulawa da aiki. Haka zalika, wannan yanayin na jefa ma’aikata cikin baƙin ciki da kuma wulaƙanci. Rashin biyan albashi na sa ma’aikatu su rasa ƙwararrun ma’aikata da kuma wahala wajen samun mai mayar da gurbinsu. Matsalar da al’umma ke fuskanta a kan rashin biyan ma’aikata haƙƙoƙin su shi ne yana janyo cece-kuce da kuma zanga-zanga wacce tana iya tada na zaune tsaye. Wannan yanayin na janyo mutane su faɗa cikin ayyukan ɓarna irin su kasuwanci almundahana, tsafe-tsafe da satar kuɗaɗen gwamnati.

Harwayau, ma’aikata su sani cewa akwai haƙƙi a kansu wajen gudanar da ayyukan nasu ta hanyar da ta dace ko da ba a biya su cikakken albashin su ko kuwa an jinkirta biyansu. Kada su biyewa sharrin shaiɗan da ruɗin zuciya. Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wa Sallama yana cewa, “Lalle Ubangiji na ƙaunar idan dayanku ya yi aiki ya inganta shi.”

Masu gidan ma’aikata su sani cewa waɗannan ma’aikatan amana ne da Ubangiji da damƙa su a ƙarƙashin su. Saboda haka, sun kyautata furucin su ya yi magana da su da kuma tabbatar masu da yanayin aiki mai kyau. Kada ka zagi ma’aikaci ko tsorata shi ko kuwa wulaƙanta shi. Ka jinjina wa ma’aikaci in ya aikata aikin a zo a gani kuma ka gyara wa ma’ikanci kura-kuransa cikin mutunci da kuma lumana.

Gwamnati ta samar wa ma’aikatan ta yanayi mai kyau da za ta taimaka masu wajen ƙaddamar da ayyukansu. Gwamnatin ta ƙara duba albashin ma’aikata domin wannan dubun saba’in ɗin da aka ƙara akan albashin ma’aikata bai taka kara ya karya ba, lura da tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin kayan masarufi da na abinci a kasuwanni. Gwamnati ta sanya tsautsararan dokoki ga duk wanda ya ci zarafin ma’aikaci.

Allah Ya tamaiki ma’aikantan mu, Ya kuma shige musu gaba a dukkanin harkokinsu. Allah Ya azurta mu da ni’imomi Sa masu albarka, Ya zaunar da ƙasar mu lafiya. Amin.HASSAN IMRAN ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]

By ukarofi