Benue: ‘Yan sanda sun fara binciken kisan ďalibar jami’a bisa kure

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Jihar Benue, ta tabbatar da mutuwar wata ďalibar ajin karshe a Jami’ar Kwararafa dake Wukari a Jihar Taraba.

Dalibar mai suna Ahenjir Emmanuella, ta rasu ne bayan wani alburushin bindigar ďan sanda ya same ta bisa kuskure.

Rundunar ta kuma umarci a gudanar da bincike mai zurfi game da lamarin, wanda ya faru a yayin binciken masu zirga-zirga.

Abokai da iyalan marigayiyar sun zargi ƴan sandan da harbe ta a lokacin da ta ke tare da abokan nata a Makurdi, Babban birnin Benue.

Lamarin ya auku ne da misali karfe 11 na safe a Shataletalen Wurukum a lokacin da ƴan sanda suke atisayen binciken masu zirga-zirga, inda suka bude wuta ga wata motar kasuwa, wadda a ciki ďalibar ta ke.

Wata ķawar marigayiyar mai suna Igbor Iorbo ta shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da ďalibar ta nufi koma wa makaranta a Wukari.

By Babaji