Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sabuwar jam’iyyar da ya koma, SDP, ta fi buƙatar ta tara mambobi daga tushe ba wai manyan ‘yan siyasa ba.
El-Rufai, wanda ya fice da ga jam’iyyar APC a watannin baya, ya bayyana hakan ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a jihar Kano a ranar Litinin.
A cewarsa, SDP jam’iyya ce da ke rajin farfaɗo da dimokuraɗiyya tun daga tushe domin gyaran Nijeriya.
“Mu ba mu damu da tara manyan ‘yan siyasa a SDP ba. Mun fi son mu ga kamar mutane miliyan 3 sun yi rijista a SDP.
“SDP jam’iyya ce da za ta bai wa kowa dama iri ɗaya. Ba za mu bari wani mutum ɗaya ya riƙa iko da jam’iyyar ba.
“So mu ke yi mu gyara dimokuraɗiyyar kasar nan,” inji El-Rufai, yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai.
Hakazalika El-Rufai ya ce SDP na da wani sashe da ke yin nazari akan cigaban Nijeriya da gyaran tattalin arzikin ƙasa da samar da tsaro idan Allah Ya sa ta samu nasara a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa yanzu ba maganar ‘yan takara ake yi ba a SDP, sai dai batun tara ‘yan jam’iyya da za su ƙarfafa ta.
