Sanatocin PDP na Osun sun nuna goyon baya ga Tinubu a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanatocin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar PDP a jihar Osun sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu a gabanin zaben shugaban ƙasa na 2027.

Sanatocin — Kamarudeen Oyewumi (Osun ta yamma), Olubiyi Ajagunla (Osun ta tsakiya), da Francis Fadahunsi (Osun ta gabas) — sun bayyana matsayinsu ne a wata sanarwa da suka fitar tare a ranar Laraba.

Goyon bayan ya biyo bayan wata ganawa da suka yi a ranar Talata.

‘Yan majalisar sun bayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu, suna ambato tarihin sa wajen jagoranci, sauye-sauyen tattalin arziki da kuma ci gaban ababen more rayuwa.

Sun yaba da shirye-shiryen gwamnatin, suna cewa akwai ci gaba a harkar tsaro da kuma raguwar farashin kayan abinci, wanda suka ce shaida ce ta ingancin manufofin shugaban kasa.

Sanatocin sun kuma bayyana alfaharinsu da daidaita kai da “tsarin hangen nesa da ci gaba na Tinubu”.

By ukarofi