PDP ta kafa kwamitin sulhu ƙarƙashin Saraki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin Amintattun babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya wato PDP ta rantsar da kwamitin sulhu mai ɗauke da mutum 20 a wani mataki na ƙara haɗa kan ‘yan jam”iyyar a matakai daban-daban na ƙasar.

Shugaban kwamitin amintattun PDP, Adolpus Wabara ya ce nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta kawo ƙarshen ka-ce-na-cen da ya dabaibaye ta tsawon lokaci, tare da ɗaukar matakai kan masu yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.Ya ce wannan matakin zai ƙara tabbatar da cewa “waɗanda ke ficewa daga jam’iyyar da ma su ne matsalar jam’iyyar,” inda ya ƙara da cewa yanzu iya halastattun ‘yan PDP ne suka rage a cikinta.

‘Yan kwamitin sun haɗa da tsohon gwaman Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Neja Mu’azu Babangida Aliyu, da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom da kuma Yakubu Garaba Lado daga jihar Katsina.

Jam’iyyar PDP ta ɗauki lokaci tana fama da rikicin cikin gida tun bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Shugaban sabon kwamitin, Abubakar Bukola Saraki ya wallafa a shafinsa na Facebook zaman taron ya yi armashi, sannan kwamitinsa zai yi aiki tuƙuru domin tabbatar da sun je babban taron jam’iyyar cikin lumana.

By ukarofi