’Yan PDP shida a Majalisar Wakilai daga Delta sun koma APC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheƙa zuwa Jam’iyya APC.

Hakazalika, wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheƙa daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP.

Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata.

Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheƙar ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma ƙasa.

Waɗanda sauka sauya sheaa zuwa APC su ne: ɓictor Nwokolo, Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Waɗanda suka bar LP zuwa PDP su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi.

Idan ba ma manta ba, a kwanakin baya ne Gwamnan Delta, Sheriff Francis Orohwedor Oboreɓwori, da tsohon gwamnan jihar kumwa tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa Ifeanyi Okowa, da wasu ƙusoshin PDP suka sauya sheƙa zuwa APC.

Ana yawan samun sauya sheƙa a Majalisar Wakilai daga jam’iyyun adawa zuwa APC mai mulki, a wannan majalisa ta 10.

By ukarofi