Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa sojojin Nijeriya, inda ya bayyana su a matsayin “jarumai, haziƙan jami’ai da masu kare ƙasa”.
Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma’ar da ta gabata a wata ziyara da ya kai jihar Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ’yan bindiga, shugaban ƙasar ya ce matsalar ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ’yan fashin daji ta jima a ƙasar.
“’Yan Nijeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Nijeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare”, inji Shugaba Tinubu.
”Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗa da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙarfin da za ku iya murƙushe duk wata barazana a ko ina ta ɓulla”.
Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu’, kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga”, inji Tinubu.
“Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Nijeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawar da matsalar tsaro a Najeriya,” inji shugaban ƙasar.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya tabbatar da tallafa wa rayuwar waɗanda ayyukan ta’addanci ya shafa.
