An kashe mutum 227 a jihohi uku cikin wata huɗu – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A cikin watanni huɗu wasu jihohi uku na Nijeriya sun faɗa cikin tashe-tashen hankula, inda suka fuskanci munanan hare-hare har sau 26, yayin da wasu 227 suka mutu a hannun ‘yan ta’adda, kamar yadda wani bincike da jaridar ɓanguard ta gudanar ya nuna.

Kashe-kashen dai ya faru ne a jihohin Borno da Adamawa da Yobe, inda ‘yan Boko Haram da mayaƙan ISWAP ke kai hare-hare amma da alama Borno ta fi ƙamari.

Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro sun ce an kashe ‘yan ta’addan da dama da ke gudanar da ayyukansu a daidai lokacin da hukumomin jihohi ke ikirarin cewa rashin tsaro na ƙara ta’azzara.

Rahotannin da aka yi nazari sun nuna cewa, aƙalla sojoji shida ne ‘yan ta’adda suka kashe a yankin.

Rahotanni sun ce waɗanda aka kashe sun haɗa da Kwamandan Sojoji, Kyaftin da sojoji 22. Haka kuma an kashe ‘yan sanda biyu da kuma ‘yan ta’adda aƙalla 36.

A halin da ake ciki, kusan 100 daga cikin waɗanda aka kashen manoma ne da masunta.

Wasu masu sharhi kan harkokin tsaro sun alaƙanta wannan lamari da sake tura jiragen Super Tucano, da kai hari da jirage masu saukar ungulu da wasu jiragen yaƙi daga yankin Arewa maso Gabas domin tunkarar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma yayin da wasu ke ikirarin cewa hakan ya faru ne sakamakon lallausan kan iyakokin yankin da makwabtan yankin tafkin Chadi wanda ke ba da damar kutsawa ‘yan ta’adda daga Nijar da Chadi da sauransu.

Hare-haren da suka sake kunno kai, ba wai kawai ya yi sanadin kashe ɗaruruwan mutane ba, tare da ruguza tsarin soji, wanda ya kai ga kwace makamai da alburusai da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP suka yi, lamarin da ya kai ga lalata dukiya.

Daga cikin manyan ‘yan Nijeriya da lamarin ya firgita har da Sanata Mohammed Ali Ndume wanda gundumar Borno ta Kudu a cewarsa ta aka sake mamaye ta.

By ukarofi