Jerin gwamnoni bakwai da suka fice daga PDP zuwa APC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori a ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a hukumance.

A shekarun baya dai wasu gwamnoni da dama sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a lokacin da suke kan mulki.

Ga jerin gwamnoni bakwai da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC:

1. Sheriff Oboreɓwori (Delta State):

Sheriff Oboreɓwori ya ba wa mutane da yawa mamaki bayan ficewa daga PDP zuwa APC a ranar Laraba. Ficewar sa ya nuna gagarumin sauyi a siyasance a Delta, wadda jiha ce ta PDP tun shekarar 1999.

2. Daɓe Umahi (Jihar Ebonyi):

Umahi ya koma APC ne a watan Nuwamba 2020 a wa’adi na biyu na gwamna. Ya ba da misali da mayar da yankin Kudu maso Gabas saniyar ware da PDP ta yi sannan ya yaba da yadda APC ta mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa a ƙarƙashin Shugaba Buhari.

3. Ben Ayade (Jihar Kuros Ribas):

Gwamna Ayade ya bar PDP zuwa APC a watan Mayun 2021. Ya ce ya yanke shawarar ne saboda son haɗa kai da gwamnatin tarayya don jawo ƙarin ayyukan raya ƙasa zuwa jihar Kuros Ribas.

4. Bello Matawalle (Tsohon gwamnan Jihar Zamfara):

Matawalle ya koma APC ne a watan Yunin 2021. Yunƙurin nasa ya biyo bayan tashe-tashen hankulan siyasa a Zamfara kuma ana kallonsa a matsayin wata dabarar ƙawance don wanzar da kwanciyar hankali da mulki.

5. Aminu Tambuwal (Jihar Sakkwato):

Tambuwal dai ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC gabanin zaɓukan 2015, ya koma PDP a 2018, daga baya kuma aka alaƙanta shi da sabon komawarsa APC tun yana kan karagar mulki, wanda hakan ke nuna zafafan siyasar sa.

6. Aliyu Wamakko (Jihar Sakwkato):

Wamakko ya koma APC ne a shekarar 2014 a lokacin yana gwamna. Yana daga cikin waɗanda suka sauya sheklƙa tun farko da yunƙurin su  taimaka wa jam’iyyar APC ta lashe zaben 2015 a lokacin.

7. Abdulfatah Ahmed (Jihar Kwara):

Ahmed, Gwamna daga 2011 zuwa 2019, ya koma APC a 2014 tare da Bukola Saraki a lokacin “Guguwar siyasa” a Kwara. Ko da yake ya koma PDP daga baya, sauya sheƙa a lokacinsa na da matuƙar muhimmanci.

By ukarofi