Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu yara biyu da aka tsinto su na kwana a titi ya karaɗe ‘social media’. Yawancin mutane na ta yaba wa wannan ƙoƙari na gwamna, amma mene ne abin burgewa a ciki? Ga duk mai shekaru irin namu, ya san cewa wannan ɗabi’ar sabuwa ce ta zamani, domin a shekarun baya babu wanda za ka samu ya na kwana a titi face mahaukata ko ’yan ƙwaya. Amma duk wani mutum, komai rashin gatansa, ya na da inda ya ke kwana. A unguwanni za ka sami soraye manya da ke zama wajen kwanan almajirai da baƙi, wani lokaci ma har masallatai na karɓar baƙuncin baƙi.
Bahaushe na da hadisinsa cewa, “ɗa na kowa ne”. Don haka babu yadda za a yi ka ga wani mai ƙaramin shekaru ya kwana a titi, ko manya sai dai waɗanda suka faɗa ajin mahaukata ko yan ƙwaya. To, amma yanzu Allah kaɗai ya san yawan mutane manya da yara da ke kwana a titi. Me ya jawo haka?
Idan na taƙaita akan yara masu kwana a titi, dalilai suna da yawa, kama da mummunar ɗabi’ar bara, wacce malamai da iyayen zamani su ka assasa, wacce a baya ba haka abin yake ba. Wato a da za ka samu duk wanda za a tura bara wani gari, za ka tarar shekarunsa sun isa ya yi noma, wato daga 12 zuwa abinda ya yi sama, saɓanin yanzu da za ka ga yara ’yan shekaru huɗu ko biyar. Iyaye su na son su yi ta aure su na haihuwa, amma ba sa son ɗaukar ɗawainiyar ’ya’yansu. Malamai na son su tara ɗalibai birjik, domin samun kuɗaɗe hannun iyaye, samun sadaka da waɗanda za su yi musu hidima ta aiki ko noma. Don haka iyaye ke watsa wa malamai nauyinsu, su kuma malamai su watso wa al’umma.
Dalilin wannan tabi’a, tare da waccan halayya ta haihuwa barkatai, ya sa Arewacin Nijeriya ta zama hedikwatar yaran da ake kira ‘out of school children’, wanda a yanzu ƙididdiga ke nuna cewa sun kai miliyan 15.3, inda Arewa maso Yamma ke da miliyan 5, sannan Kano ke zama jagaba da sama da miliyan ɗaya.
To, don Allah don gwamna ya tsakuro yara biyu har wani abin yamaɗiɗi ne? Na farko dai a matsayinsa na gwamna ya na da gagarumar gudunmuwa da zai iya bayarwa fiye da haka a hukumance. Akwai maƙalar da na gabatar kusan shekaru huɗu a baya a babban taro kan almajiranci (Almajiri Summit) a Arewa House, inda a ciki baya ga bibiyar tarihin almajiranci tun daga lokacin Manzo (SAW) har zuwan Turawa, na bayar da shawarwarin hanyoyi na zahiri da za a iya gyarawa da amfanar da harkar maimakon ta ci gaba da zama nauyi ga al’umma.
1. Ta fannin shari’a gwamnati na iya amfani da majalisa ta yi doka, don hana yara masu ƙarancin shekaru zuwa almajiranci. Idan aka tsayar da shekaru sai aƙalla 12 zuwa sama za a iya tura almajiri karatu, kuma kada yaro ya wuce jiharsa, nan take ka zabge kashi 50% ko fiye da haka na masu bara.
2. Gwamnati ta gyara firamare yadda yara za su iya samun karatu ingantacce kyauta.
3. ƙirƙirar makarantun tsangayu, kamar yadda tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi, a ba su kulawa yadda almajirai kafin kammalawa sun iya sana’o’i da za su dogara da kansu, kuma tsangayun za su zama hanyar sama wa al’ummar da suke ciki ababen buƙatu cikin sauƙi (sabulu, mai, ‘pure water’, ɗinki, takalma, jakunkuna da sana’o’i iri-iri, noman rani da saurasnu), yadda za su zama wani ‘manufacturing hub’ kenan. A cikin wannan sati Kano ta ƙaddamar da aikin sake gina majalisar dokokin jihar akan Naira biliyan 40. Kanawa ba sa buƙatar wannan aiki, kuma idan za a saka wannan kuɗi a aikin gina tsangayu, ana iya samar da tsangayu biyu a kowacce local goɓernment (88 kenan) akan Naira miliyan 450, wacce za ta ɗauki almajirai 500 duk tsangaya. Kun ga za a kwashe almajirai 44,000 kenan daga titi a samar musu wajen kwana da abin sana’a.
Sannan masu hannu da shuni su assasa gina gidajen marayu waɗanda su ma za a koyar da sana’o’i, da assasa yin waƙafin gidajen kwana na baƙi ko waɗanda ba su da wuraren kwana.
A lokacin Korona babban attajirinmu, Abdussamad Rabiu, ya bayar da katafaren rukunin ginin ofisoshinsa akan titin ‘Court Road’, don killace masu Korona, amma wajen na nan har yanzu a yashe babu mai amfanarsa tsawon waɗannan shekaru. Me zai hana gwamna ya roƙi Abdussamad ya bayar da wajen ga gwamnati ta saka gadajen kwana da buɗe ajijuwa a ciki a riƙa saka irin waɗannan yara da gwamna ya samo guda biyu, maimakon wajen ya yi ta zama a banza ba mai morarsa?
Kwanan baya a wajen taron ƙaddamar da littafin IBB, Aliko Dangote, ya sayi littafin na Naira biliyan 8, shi kuma Abdussamad ya sayi na Naira biliyan 5, a junansu sun yi wa IBB cinikin Naira biliyan 13 kenan, wanda ba ya buƙatarsu. Me zai hana su biyun su yi wata gidauniya irin haka, domin gina gidajen marayu da tsangayu na zamani domin sama wa almajirai sana’oi tare da samar wa al’ummomi kayan buƙatu? Idan suka samar da irin waɗannan tsangayu mutum nawa za su sami ayyukan yi kama daga koyo da koyarwa da samar da wani ‘manufacturing base’ ga al’ummar da aka yi tsangayar a wajen? Ta haka fa China ta mamaye manufacturing a Duniya. Shi yawan jama’a alheri ne matukar akwai shugabanci mai kishin al’ummar da zai tallafawa mutanenta su zama masu dogaro da kansu. Almajiranmu, mu na iya mayar da su hanya ta manufacturing din ababen bukatu a kowacce local goɓernment, yadda maimakon zama nauyi a kan al’umma sai su zama abin dogaron al’umma.
Ina ganin kalubalen Gwamna ke nan a yanzu, na bin irin wadannan hanyoyin domin magance matsalar bara, kwanan titi da rashin ayyukan yi. Ya na da damar da a yanzu zai iya zunguro wadannan hanyoyin domin ganin an sami canji na zahiri a kasa wanda zai habaka tattalin arzikin jihar Kano. Ba tsinto Yara guda biyu a yi ta hoto da su ana yadawa ba, domin Rana ita yau iwar haka, wani zancen ake ba wannan ba. Lokaci a kullum kurewa ya ke yi mana, kuma alherin da muka yi tsakani da Allah, shi kadai ne abu me dorewa da za mu yi alfahari da shi wata Rana.
Gwamnatin Tarayya a nata kokarin ta kafa hukumar Almajiri Commission, kuma Dan Kano ne Chairman a yanzu. Wace irin alaka gwamnatocin Kano da Tarayya su ka yi don morar wannan hukumar ganin yadda Kano ke kan gaba a yawan almajirai?
Kamar yadda Bahaushe ya ce “ɗa na kowa ne” abin nufi shine dole kowane Uba ya dauki nauyin abinda ya haifa domin shi Allah zai fara tambaya. Gwamnati kuma dole ta dauki nauyin ilimintar da al’ummarta da sama musu ayyuka. Su kuma Attajirai wajibi zakkarsu da tallafinsu ya karkata ga masu rauni a al’umma (Kuma ba wanda ya ke da raunin almajirai a yau), ba su riki ayyukan riya ba, sannan ita kuma al’umma ta tashi tsaye wajen tarbiya da taimakon juna daidai gwargwado. Ta haka, za a iya fara diffusing din bom din yawan jama’a da Arewa ke tarawa kanta. Bom din da tuni ya fara fashewa ya na jeho mana Fulani Yan ta’adda, Yan Boko Haram da kidnappers. Wa ya san me zai zo nan gaba idan ba’a dauki kyakkyawan mataki ba? Allah ya kyauta.
