Nijeriya ta sauke bashin tiriliyan N2.59 na IMF

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Nijeriya ta biya Dala Biliyan 1.61 (kimanin Naira Tiriliyan 2.59) da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ke bin ta.

Wani bincike na shafin yanar gizon IMF na IntelRegion a ranar 7 ga Mayu, 2025, ya nuna cewa an cire Nijeriya cikin jerin ƙasashen IMF ke bi bashi.

Wani bayani da ya samu shahararriyar kamfanin bayanai, StatiSense ya nuna cewa Nijeriya ta biya bashin sannu a hankali daga Dala biliyan 1.61 a watan Yuli 28, 2023 zuwa dala biliyan 1.37 a ranar 5 ga Janairu, 2024 zuwa dala miliyan 933.03 a ranar 10 ga Yuli, 2024 zuwa dala miliyan 472.06 a ranar 8 ga watan Janairu, 2025, kuma ta gana biya dukkkan bashin.

Wata sanarwa da hukumar ta IMF ta fitar da ke tabbatar da ci gaban ta ce, matakin ya kawo ƙarshen matsalolin kuɗi da aka shafe shekaru da dama ana fuskanta wanda ya yi nauyi kan ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

By ukarofi